Gobe za a ƙaddamar da littafin ‘100+ questions before Nikkah’

Daga AISHA ASAS

Shahararriya kuma ƙwararriyar mai bayar da shawarwari kan zamantakewar aure da kuma rayuwa bakiɗaya, Khadija Ibrahim, marubuciya da ta jima tana gyara al’umma da alƙalaminta, ta shirya tsaf don bayar da ƙarin gudunmawa ga masu shirin yin aure, wato littafin da zai amsa tambayoyi ɗari har da ɗori da mata da maza suke buƙatar sani kafin su shige daga ciki.

Littafin mai suna tambayoyi ɗari da ɗori kafin aure, wanda zai kasance a turance, wato ‘100+ questions before Nikkah’ zai amsa kusan dukkan tambayoyin da ake buƙatar sani game da aure, waɗanda za su fitar da samari da ‘yan mata masu shirin yin aure daga duhu kan sha’anin aure da abinda ya ƙunsa.

Mai girma gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal ne babban baƙo na musamman, yayin da Shaik Abu Mazeedatul Khaiyr bin Rauf, zai jagoranci ƙaddamar da littafin. Baqo mai jawabi, Ustaz Dakta Abulfattah Adeyeme, yayin da tsohuwar ministan jinƙai, Hajiya Sadiya Umar Faruk za ta ƙaddamar da littafin. Mai girma Barden Kudu Zazzau, Malam Bashir Abubakar MFR zai kasance uban taron.

Za a ƙaddamar da littafin a gobe, Asabar, 14 ga watan 10, shekarar 2023, a Babban Zauren Taro na Masallacin Ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 10 na safe.