Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun yi garkuwa da wani malamin addinin Islama, Alfa Fasasi Ola Mejabi da ƙaninsa a Jihar Kogi.
Malamin da sauran su su na miƙa ɗauke da gawar babban Limamin Ayegunle Gbede, Sheikh Musa Olorunkemi, daga Lokoja zuwa Ayegunle Gbede da ke ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi domin yi masa jana’iza a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka yi karo da masu garkuwa da mutane.
Ɗaya daga cikin mutanen da ke cikin motar da suka tsallake rijiya da baya ya shaida wa manema labarau cewa, lamarin ya faru ne a Oshokoshoko kan hanyar Lokoja-Obajana-Kabba.
Ya bayyana cewa, motarsu na tafiya gaban motar da ke ɗauke da gawar marigayi Sheikh Musa, wanda ya rasu a safiyar Lahadi bayan gajeriyar rashin lafiya.
Wata majiya ta shaida wa rahoton Kogi cewa an kashe layukan wayar waɗanda abin ya shafa tun bayan sace su, amma ta ƙara da cewa, masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi iyalan a safiyar ranar Litinin inda suka buƙaci a biya su Naira miliyan 10 domin a sako su.
Mai bai wa jihar shawara kan harkokin tsaro, Commodore Jerry Omadara, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jami’an tsaro a jihar na yin duk mai yiwuwa don kuvutar da su daga kogon masu garkuwa da mutane.
“Gaskiya ne amma jami’an tsaro na kan hanyarsu domin kuɓutar da su tare da cafke masu garkuwa da mutanen,” ya tabbatar.
