Mutum 20 sun mutu sakamakon ɓarkewar cutar Mashaƙo a Kaduna

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Aƙalla mutane 20 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon ɓarkewar cutar Mashaƙo a Jihar Kaduna.

Babban babban Jami’in hukumar kula da lafiya a matakin farko na ƙasa, Dakta Faisal Shuaibu ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, inda ya ce an samu mutum 156 waɗanda suka kamu da cutar a jihar.

Da yake zantawa da manema labarai a cibiyar kula da cutar mashaƙo ta jihar Kaduna da ke asibitin koyarwa na Barau Dikko a babban birnin jihar, Shu’aibu ya buq’ƙaci jama’a da su bi ƙa’idojin kiyayewa da aka gindaya, su kuma lura da alamun cutar domin samun kula cikin gaggawa.

“Jihar Kaduna tana mataki na shida, cikin jihohi bakwai da suka fi yawan masu cutar Mashaƙo,” inji shi.

“Tun a Maris da aka fara samun ɓullar cutar a Kaduna, mutane 156 suka kamu da ita sannan kusan mutane 20 ne suka mutu.”

By Editor