Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi sabbin naɗe-naɗen muƙamai biyar a wasu hukumomin da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Sadarwa, Ƙirƙire-Ƙirƙire da Tattalin Arziki na Zamani ta Tarayya, a ranar Laraba.
Waɗanda aka naɗe su ne Aminu Maida, wanda ya taɓa zama Babban Darakta na Fasaha da ayyuka a Nijeriya ‘Inter-Bank Settlement System Plc’ (NIBSS), wanda yanzu ya naɗa Mataimakin Shugaban Hukumar (EVC) a matsayin Shugaba na Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC).
An sake naɗa Shugaban Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) Kashifu Inuwa Abdullahi a karo na biyu.
A cewar wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaba Tinubu ya kuma naɗa Idris Aubankudi a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin fasaha da tattalin arziki na zamani.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin sabbin shugabannin zartarwa a faɗin hukumomi da dama da ke ƙarƙashin ma’aikatar sadarwa, ƙirƙire-ƙirƙire, da tattalin arzikin dijital ta tarayya.
