Tun daga lokacin da aka ayyana janye tallafin fetur mutane suka shiga mawuyacin hali, saboda ba wani matakin gaggawa da aka ɗauka don nunawa gwamnati matsalar da za a shiga. Ɗaukar matakin gyara da wuri ya fi komai. Na fahimci hakane a lokacin wani rikicin aƙida da wata mata ta taɓa haddasawa a Bauchi. Kwamishinan ’yan sanda na lokacin ya kira ’yan jarida ya faɗa mana mace ta haddasa rigimar amma bai san inda ta ke ba.
Daga lokacin na fara bincike zuwa matuary a asibitin TH, saboda can aka kai gawarwaki kusan 40 da aka kashe lokacin rikicin aka jibge.
Misalin ƙarfe goman dare na je na tsara mai gadin matuary ya buɗe mana da abokina ɗan jaridar RFI daga Kano ya zo muka shiga muka duba gawarwakin rikicin babu mata cikin su.
Da safe na tafi inda aka tsugunar da mutanen da ke hijra na ci gaba da bincike, zan tafi bayan na gama hira da mutane sai wasu mata suka ce na rage musu hanya na ɗauko su a mota suna hira sai naji sun ce saboda ita zananniya ce wasu ƙungiyoyi sun tserar da ita an kashe mana maza an kama mana yara an tsare ita ta gudu.
Daga nan suka ƙara min bayani na bi na samu shugabannin ƙungiyoyi da suka zarga da fitar da ita ba yadda ba su yi ba na rufa musu asiri na ƙi karɓan duk wani tayi da suka yi min na ce sai hukuma ta ji. Sai na kira kwamishinan ’yan sanda na ce ina son ganinsa ya ce na zo yana ofis.
Na ba shi duk bayanan da suka dace nan take ya gayyato na ƙasa da shi ya ce ga labarin da ɗan jarida ya kawo masa. Nan take ya haɗa motoci biyu cikin dare aka tafi can wata jiha aka ɗauko matar aka jefa ta gidan yari na tsawon lokaci.
Tun daga nan wani mataimakin kwamishina Tsafe ya zama abokina har gidana yake zuwa ina zuwa gidansa. Wani lokacin idan suka nemi bayanin abin da ke faruwa ba su gano ba yakan nemi taimakona na taya su bincike.
Saboda mutane sukan yarda da ɗan jarida su bada bayani fiye da ɗan sanda. Domin gani suke ɗan sanda kama su zai yi.
Daga Muazu Hardawa Edita Jaridar Alheri a Bauchi. 08062333065.
