Duwatsun Falasɗinawa da boma-boman Yahudawa

Spread the love

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Zubar da jinin Falasɗinawa daga ƙarfin sojan Isra’ila ba wani sabon abu ba ne. Tun lokacin da Isra’ila ta samu galabar a yaqi da ƙasashen Larabawa a 1967 a ke ta samun mamaye yankunan Falasɗinawa ba ƙaƙƙautawa kuma ya zama tamkar a jefe ka kashin awaki ne kuma a hana ka kuka. Ai aƙalla kuka kan ragewa mutum baƙin ciki kuma takaici. Shekaru gommai da su ka wuce a kan ga ’yan yaran Falasɗinawa na ɗaukar duwatsu su na jifar sojojin Isra’ila da ke cikin tankokin yaƙi.

Kowa ya san sakamakon mai dutse ya jefi mai igwa. An ma yi zargin hatta shugaban Falasɗinawa na gwagwarmaya Yasser Arafat ya ci karo da makirci ne har ya yi sanadiyyar rayuwarsa. Ka ga duk yanda Arafat ya yi ta ƙoƙarin sulhu da Yahudawa da zama a lokuta daban-daban da manyan ƙasashen duniya, amma haka ya kwanta dama ba tare da nasarar hana kisan gilla ga mutanen sa ba.

Ai kwanakin baya ma ’yar jarida da ke aiki da gidan talabijin na Aljazeera daga yankin Falasɗinawa Shireen Abu Akleh ta rasa ran ta bayan harbe ta da sojojin Isra’ila su ka yi. An ta magana kan kisan amma ba wanda a ka hukunta sai dai kawai a ƙarshe a ke cewa ba mamaki cikin kuskure albarsushi ya yi batan kai ya same ta. Duk wani fitaccen ɗan gwagwarmayar neman ’yancin Falasɗinawa ba ya kai wa labari wa aimma a kashe shi ko kuma ya tafi gudun hijira.

Hakanan wani yanayin kuma ko ya yi ta zama cikin barazana ko a kama shi a jefa gidan yari. Za a iya tunawa da dattijon ’yan Hamas Sheikh Ahmad Yassin ya rasa ran sa bayan jirgi mai saukar angulu ya harba ma sa makami mai linzami lokacin da a ke tura shi kan keken guragu don tafiya sallar asuba a 2004. Masu tsaron lafiyar sa biyu ma nan su ka rasa ran su.

Wato Isra’ila za ta iya ɗaukar jirgin yaqi ta tafi farautar mutum daya kuma za ta iya kashe shi da duk waɗanda ke kewaye da shi. Shi kan sa shugaban Hams Ismail Haniyeh ya tava tsallake rijiya da baya-bayan harbo makami don hallaka shi. A takaice dai mamaye yankin Falasɗinawa da Yahudawa su ka yi bisa muradun Birtaniya da mara bayan ƙasashen Turai ya jefa Falasɗinawa a cikin uqubar zama tamkar bayi a ƙasar su ta gado.

Komai na su na rayuwa ya na hannun gwamnatin Isra’ila. Bisa siyasar duniya ƙasashen Larabawa su kan mara baya ko kuma a ce su kan yi hulɗa da ƙasar Isra’ila inda maraya bayan su ga ’yan uwan su Falasɗinawa ya kan zama na fatar baki ne. Gwamnatin Falasɗinawa na birnin Ramallah ne inda shugaba Mahmud Abbas ya ke da zama da sauran manyan Falasɗinawa waɗanda Isra’ila ba ta aunawa da makamai.

Yankin Gaza kuma nan ’yan gwagwarmayar Hamas su ke kuma a nan ne hare-haren Isra’ila su ka fi karkata don duniya ta zayyana ’yan Hamas a matsayin ’yan ta’adda. An haƙiƙance faɗan da ya ɓarke na yanzun nan ya taso ne yayin da jami’an gwamnatin Isra’ila su ka matsa ƙaimi wajen keta haddin masallacin Baitul Mukaddas a birnin Kudus. Fiye da sau ɗaya ministan tsaron Isra’ila Itamar Ben Givir ya shiga harabar masallacin da rakiyar jami’an tsaro.

Wannan na zama tsokana ga Falasɗinawa da kuma Musulmin duniya gaba ɗaya. A zamanin mulkin tsohon shugaban Amurka Donald Trump an samu wani haɗin kan diflomasiyya tsakanin manyan ƙasashen Larabawa da Isra’ila da a ka raɗawa suna “ABRAHAM ACCORD PEACE TREATY” da ke nuna ƙasashe masu tarihi da Annabi Ibrahim Alaihis Salam su hada kai don zaman salama da juna da kuma alaƙar tattalin arziki.

A lokacin Falasɗinawa sin yi Allah wadai da yarjejeniyar da kuma nuna takaicin yadda su ke ganin ’yan uwan su Larabawa sun ci amanar su. Shugaban Turkiyya wanda Balarabe ba ne Raceb Tayyeb Erdoan shi ya marawa tafiyar Falasɗinawa baya.

Masu sharhi kan fitinar da ta ɓarke tsakanin Isra’ila da ‘yan Hamas na ƙarfafa tunanin Majalisar Ɗinkin Duniya ce ke da haƙƙin shiga tsakani don kawo sulhu.

Batun rikicin na Palasɗinawa da Yahudawa na daga abun da ke ɗauke hankalin mutane a Nijeriya cikin lamuran ƙasashen duniya.

Isra’ila da ke da hulɗar jakadanci da Nijeriya na da wasu yarjeniyoyin tsaro da Nijeriya, kuma duk shekara dubban mabiya addinin Kirista a Nijeriya kan kai ziyara Urshalima a garuruwan Israila, yankin Palasdinawa, Jodan, tuddan Golan da ma cikin Masar don addu’a a sassan tarihi da ke da nasaba da Yesu Almasihu.

A sharhin sa, Farfesa Sani Yahaya ya ce tura ce ta kai bango ya sa ‘yan Hamas turjiya amma shiga tsanaki a yanzu shi ne mafi a’ala “Wannan akasi kowa ya sani a duniya an daɗe a na yi, ga shi nan yanzu ya kawo mugun asarar rayuka. Majalisar Ɗinkin Duniya ta zauna ta yi adalci.”

Fasto Simon A.S wanda sakataren ƙungiyar Kiristoci ne na jihohin Arewa ta tsakiya ya ziyarci Isra’ila sau da dama ya na mai cewa faɗan ya so ya wuce na harshe da haƙori ne tsakanin ‘yan uwa na tarihi “na je na ga Musulmi, Kirista da Yahudawa na zaune tare kuma wani mabuɗin wajen ibadar mabiya addinin Kirista ma na hannun Musulmi ne.”

Shi kuma shaharerren shugaban ƙungiyar matasa ta Nijeriya Komred Murtala Garba ya buƙaci matasan sassan biyu su yarda gora don duniyar yau ba ta kyautata ko kawo riba da zaman kiyaiya.

Haƙiƙa akwai masu marawa Falasɗinawa baya a Nijeriya da kuma masu ƙaunar Isra’ila da yiwuwar ba wa kowane ɓangare uzuri a irin wannan yanayi na zubar da jini.

Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da ziyarar ibada Urshalima biyo bayan kaurewar faɗa tsakanin Falasɗinawa ’yan ƙungiyar Hamas da sojojin Isra’ila.

Rukunin masu ziyarar ibadar na 5 a bana daga jihar Lagos da ke ɗauke da mutum 350 ya dawo gida lafiya bayan ziyartar sassan ibada yayin da a ke barin wuta a yankin Gaza.

Babban sakataren hukumar ziyarar ibadar Reverend Yakubu Pam ya ce kimanin mutum 50 ne daga Lagos ba su samu tafiya ba gabanin dakatar da ziyarar kuma za a koma tafiya da zarar salama ta samu.

Reverend Pam ya ƙara da cewa, ziyarar kan shafi cikin Isra’ila da Jodan don haka masu ibadar su ka takaita ga arewacin Israila inda ba a arangama “wuraren da mu ke tafiya na ta arewa a Israila, kuma Allah ya sa rikici bai same su ba domin Gaza na da nisa daga inda su ke. Sun yi tafiyar su, sun duba wurare da za su yi ibadar su ba damuwa.”

A nasa sharhin kan fitinar ta Yahudawa da Falasɗinawa sakataren ƙungiyar Kiristoci reshen Arewa ta tsakiya Simon A.S Dolly ya ce cika alƙawarin manzanci ne a littafi mai tsarki da ke buƙatar neman sauki daga Allah.

A gefe guda malaman Islama na kira ga samun adalci a matsayin hanyar kawo ƙarshen fitinar ta shekaru aru-aru.

Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya ce fitina ba ta kawo wata riba ga jama’ar da ke zaune a yanki ɗaya “mu na kira ga jama’a a cigaba da tayawa da addu’a don samun zaman lafiya.”

Kamar yadda Saudiyya ke da muhimmanci ga al’ummar Nijeriya musamman Musulmi don aikin hajji, hakanan Israila da yankin Falasɗinawa ya ke ga Musulmi, Kirista da ma masu wata aqidar da ta saba da waɗannan don masallacin BAITUL MUKADDAS da ke da daraja ga Musulmi, Kirista da Yahudawa.

Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya bugawa Yarima Muhammad bin Salman waya inda su ka tattauna kan rikicin da ya varke tsakanin Falasɗinawa da Yahudawa.

Wannan shi ne karo na farko da shugabannin biyu ke magana ta waya kasancewar zaman doya da manja da ke tsakanin ƙasashen su biyu.

In za a tuna Saudiyya da Iran sun dawo da hulɗar jakadanci bayan shiga tsakanin ƙasar Sin inda har ma su ka buɗe ofisoshin jakadancin da su ka daɗe a rufe ruf.

Ministan wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya ziyarci babban birnin Iran Tehran inda shi ma ministan wajen Iran Amir Hossein Aabdollahian ya ziyarci birnin Riyadh.

A zantawar wayar, Yarima Muhammad ya ba da tabbacin ɗaukar duk matakan da su ka dace wajen dakatar da cigaba da zubar da jini a faɗan.

Hakanan Yariman ya bukaci lalle a riƙa bin dokokin duniya da kauce wa kai hare-hare kan fararen hula.

Saudiyya ta nanata ƙudurin mara wa Falasɗinawa baya don cimma burin su na kafa ƙasa mai ‘yanci.

Kammalawa;

Zuwa rubuta wannan shafi na alƙibla, fiye da mutum 3000 su ka rasa ransu daga Falasɗinawa da Yahudawa. Duk da Falasɗinawa su ka fi rasa mutane ciki da mata da ƙananan yara, su ma Yahudawa sun rasa fiye da mutum 1000 da ya zama mafi asara na farko a shekaru gommai.

Gaskiya ga dukkan masu ƙaunan zaman lafiya sai a taya da addu’a don dakatar da zubar da jini. Haƙiƙa ya na da kyau masu fada a ji a duniya su duba batun na Falasɗinawa da adalci don ba su damar kafa ƙasar kan su mai ’yanci da zama abun alfahari a duniya. Abun sani dai shi ne zalunci ba ya dawwama.

By Editor