Yadda cire tallafi ke ƙara haifar da gagarumar matsalar fetur a Nijeriya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Watanni biyar kenan bayan Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin fetur, yayin da ‘yan Nijeriya suka afka cikin matsananciyar tsadar rayuwa, yanzu kuma wasu gaggan matsalolin da ke sake dabaibaye hada-hadar shigo da tataccen fetur cikin Nijeriya daga daga waje, sai bijirowa suke yi su na kwankwatsar ‘yan Nijeriya, ta hanyar zaizaye masu ɗan abin da suke samu na yau da kullum.

Bayan cire tallafin fetur da lamarin ya kai ga har lita 1 ta kai N617, Gwamnatin Tarayya ta ce za ta tsame kan ta daga shigo da fetur, domin bai wa ‘yan kasuwa lasisin shigo da fetur ƙasar nan.

Tun daga 2016 dai lokacin da Buhari ya hau mulki, har cikin 2023 NNPC ne ke shigo da fetur ɗin da ake amfani da shi a Nijeriya.

Bayan cire tallafin fetur, Gwamnatin Tinubu ta bai wa wasu ‘yan kasuwa lasisin shigo da fetur, wanda hakan ya sa a ranar 19 Ga Yuli, kamfanin Emadeb Energy Services Limited ya shigo da lodin farko na fetur lita miliyan 27 cikin ƙasar nan.

Rahoton da Emadeb Energy Services ya fitar, ya nuna cewa fetur ɗin da ya sayo kuɗin sa ya zarce Dala miliyan 17.

Haka dai Shugaban kamfanin na EESL, Adebowale Olujimi ya sanar a lokacin a Legas.

Adebowale Olujimi ya ce sai dai kuma duk da cire tallafin fetur da aka yi, babban abin alheri ga Nijeriya shi ne a riƙa tace fetur a cikin ƙasar nan kawai.

Ya ce ya faɗi wannan ra’ayin ne, bisa ga tsananin tsadar da Dala ke yi, a lokaci ɗaya kuma darajar Naira sai qara tavarbarewa ta ke yi.

“Yanzu shi kan sa fetur ɗin da ke cikin wannan jirgin ruwan har lita miliyan 27, ba abu ba ne da kawai za ka je kasuwa yanzu-yanzu kai-tsaye ka sa kwano ka kamfato ba.

Kuɗin sa ya haura Dala miliyan 17. A yadda canjin kuɗi ke tashi sama, yadda za ka sayi Dala a yau, a gobe ba haka za ka same ta ba. Mafita kawai a gaskiya ita ce a riƙa tace fetur nan cikin gida Nijeriya.” Haka Olujimi ya bayyana a hirar sa da gidan talabijin na Arise TV, lokacin da ya shigo da fetur ɗin.

Wani ƙarin abin ɗaure kai shi ne yadda ake yaɗa ji-ta-ji-tar cewa gwamnatin tarayya ta dawo ta na biyan tallafin fetur, domin ta samu farashin lita ya tsaya a N617, ganin yadda darajar Naira ta ƙara taɓarɓarewa, Dala kuma ta ƙara tashi sama sosai.

Cikin watan Agusta dai Shugaba Tinubu ya ce ba za a sake ƙara wa litar fetur farashi ba.

Sai dai kuma daga baya Shugaban NNPCL, Mele Kyari ya fito ya ce ba a koma ana biyan tallafin fetur ba.

Kyari ya ce NNPCL ta koma hada-hadar fetur ne, saboda ta ha manyan ‘yan kasuwa ba su iya shigo da fetur ɗin daga waje.”

A yanzu ne ma lamarin matsalar fetur zai ƙara ta’azzara, domin darajar Naira ta karye zuwa kashi 40 bisa 100, ko ma a ce kusan 50 bisa 100.

Halin da ake ciki kamfanonin da aka bai wa lasisin shigo da fetur, ba za su iya shigo da shi daga waje ba, saboda tsadar canjin kuɗi, wanda farashin dala ya cilla sama, ita kuma naira wadda da ita ake sayar da fetur ɗin idan an shigo da shi, a kullum darajar ta sai karyewa ta ke yi.

By Editor