Raɗɗa ya yi Allah-wadai da kashe mutane 20 da ‘yan bindiga suka yi wajen taron mauludi a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya yi Allah-wadai da hallaka mutane 20 da wasu ‘yan bindiga su ka yi a Ƙaramar Hukumar Musawa ta jihar Katsina lokacin da suke gudanar da taron Mauludi.

Kazalika, gwamnan ya kuma jajentawa al’ummar ƙaramar hukumar Matazu dangane da kashe mutane biyar da wasu ‘yan bindigar su ka yi a wani harin na daban.

Raɗɗa ya bayyana haka ne a ƙaramar hukumar Musawa lokacin da ya kai ziyarar ta’aziya ga iyalan waɗanda ‘yan bindigar suka kashe a hare-haren da su kai a ƙananan hukumomin Musawa, Ɗan Musa, Matazu da Faskari.

Idan za a iya tunawa Manhaja ta kawo labarin yadda ‘yan bindigar suka afka wa wasu mutane dake taron tunawa da haihuwar fiyayyen halitta (S.A.W) da misalin ƙarfe 11 na dare inda suka kashe mutane 20 tare da jikkata wasu da dama, ɓarayin dajin sun kuma yi awon gaba da mahalarta taron mauludin zuwa cikin daji wanda har yanzu ba a san adadinsu ba.

“Na yi matuqar kaɗuwa da samun labarin kashe waɗannan mutane masu yawa haka,wanda ‘yan bindiga marasa imani su ka yi wa al’umominmu.” Inji gwamnan.

Raɗɗa ya kuma ƙuduri aniyar kakkaɓe ‘yan ta’addar a duk inda suke voye.

Ya kuma nanata cewar, gwamnatin jihar Katsina ba za ta gajiya ba, wajen ci gaba da yaƙar ‘yan bindigar domin dawo da zaman lafiya a jihar.

A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar malam Bala Salisu Zango, ya fitar ya bayyana hare haren ‘yan bindigar da cewa na ramuwar gayya ne duba da yadda a cikin ‘yan kwanakin nan jami’an tsaro da gwamnatin jihar ta kafa domin yaƙi da matsalar tsaro su ka kai a hari maɓoyar ‘yan bindigar inda suka samu nasarar hallaka da dama daga cikinsu.

By Editor