Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A makon da ya gabata wasu rahotanni masu ɗaga hankali sun fito daga Jihar Taraba, inda aka rawaito wani ɗalibi ya daɓa wa malaminsa wuƙa a ciki, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Washegarin ranar da wancan al’amari ya faru kuma wani ɗalibin Jami’ar Jihar Taraba ya yanka wani ɗalibi ɗan uwansa a wuya, wanda shi ma ya yi dalilin mutuwarsa. Duk a cikin wannan makon, wasu hotuna marasa daɗin gani sun fito daga wannan jihar dai, inda ake nuna wasu ɗalibai mata da suka kammala samun Diploma a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Taraba da ke Jalingo, sun fito suna abin al’adar nan da ɗalibai kan yi bayan gama karatu suna rubuce-rubuce a jikin rigunansu, don yin bankwana.
Amma sai ga waɗannan ɗalibai mata sun cire rigunansu da wandunansu, ana musu wannan rubutu a jikin rigunan mama da ƙananan wandunansu na ciki, wato kamfai, babu kunya babu tsoron Allah, duk da sunan murnar kammala karatu.
Ko da makonnin baya da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ƙaddamar da samamen kawar da ayyukan baɗala da alfasha a cikin garin, da dama waɗanda aka kama a bakin otel-otel da wuraren shaƙatawa ’yan mata ne da suka bayyana kansu a matsayin ɗalibai daga wasu manyan makarantun da ke jihar, waɗanda suka yi ikirarin sun je ne sayen abinci ko kasuwanci.
Amma bayanan da ke fitowa daga bisani sun tabbatar da ayyukan da waɗannan ’yan mata ko matasa ke yi ba abubuwa ne da suka kamata a samu ɗalibi ko ɗaliba suna yi ba, musamman sanin cewa, iyayensu sun tura su ne don su yi karatu su samu ilimi da zai taimaka musu su riƙe kansu kuma su kare mutuncinsu.
Abin takaici ne matuƙa a ce ganin yadda manyan cibiyoyin ilimi na ƙasar nan da suka haɗa da jami’o’i, kwalejojin kimiyya da fasaha, kwalejojin ilimi, makarantun koyar da aikin jinya da sauran manya-manyan cibiyoyin ilimi, inda ake sa ran matasa za su samu ingantaccen ilimi da kyakkyawar tarbiyya, amma sai ka ga rayuwarsu ta gurɓace da wasu baƙin halaye da ko a gaban iyayensu ba sa iya yi. A makaranta ne za ka ga gungun matasa sun zama ’yan ƙungiyar asiri, suna shaye-shaye da amfani da makamai wajen yin fashi ko sace-sace, da yi wa ’yan mata fyaɗe. Ko kuma ’yan mata masu bin maza da sayar mutuncinsu saboda wani ɗan kuɗi da za a basu su sayi kayan shafe-shafe ko sutura da abincin ƙwalama a makaranta.
A makaranta ne ɗalibi zai riƙa yi wa malamansa barazana sai sun bashi irin makin da ya buƙata ko kuma ƙoƙarin amfani da makami saboda sun haɗa budurwa da malamin, ga kuma yawan kai wa malamai maza hari da ’yan mata ke yi, suna yaudararsu da fasiƙanci don su basu makin da zai sa su samu sakamako mai kyau.
Mun sha ganin yadda jami’an ’yan sanda ke bayyana yadda suka yi nasarar kamen wasu ɓatagari da ake zargi da laifi wajen aikata wasu munanan laifuka. Abin takaici da mamaki sai ka ga daga cikin ɓarayi ko ’yan fashin da aka kama akwai ɗalibai daga wasu jami’o’i ko manyan makarantu. Wannan abu ne mai matuƙar karayar da zuciya da kashe gwiwar kowanne uba ko iyaye da yaransu ke karatu, a kusa ko nesa da su.
Abin ne mai matuƙar ɗaga hankali, yadda wannan lalacewa ta wuce manyan makarantu har zuwa makarantun sakandire. Kamar labarin farko da na bayar na yaron da ya kashe malaminsa a makatantar sakandiren gwamnati da ke Jalingo.
Yara ƙanana da ke cikin shekarun tashen balaga sun zama ’yan daba, ko gaggan varayi, ’yan shaye-shaye, ko karuwai masu bin maza. Yayin da sauran waɗanda Allah Ya tsare daga cikinsu suke cikin rashin tsaro da fargabar abin da zai je ya zo, saboda suna rayuwa cikin marasa gaskiya da tarbiyya. Karen wata ɗaliba ce da ta yi karatu a wata makarantar sakandiren kwana a Abuja, amma ta gamu da ajalinta a dalilin fyaɗe da wasu gungun ɓatagari suka yi mata.
Sakamakon binciken da likitoci suka yi sun gano cewa, ta rasa ranta ne a dalilin wata ƙwayar cuta da ta kamu da ita, wacce ake ɗauka daga masu jima’i barkatai, bayan an yi mata fyaɗe, wanda ya lalata mata gabanta da duburarta.
Wani rahoto daga Jihar Legos ya bayyana yadda wasu ɓatagari da ke Kwalejin Dowen suka kashe wani ɗalibi Sylvester Oromoni ɗan shekara 12 bayan sun nemi ya sha wani tsumi da ake zargin na tsafi ne, don su shigar da shi ƙungiyarsu ta asiri, ya ƙi yarda. Wannan ya biyo bayan wani bidiyo da aka yi ta yaɗawa a kafafen sadarwa inda ake nuna wasu ɗalibai masu ƙananan shekaru suka ɗauki kansu suna iskanci, ba tare da sun ɓoye kansu ba.
Zarge-zarge suna yawa kan ɗalibai mata da ke karatu a jami’o’i da manyan makarantu kan irin rayuwar banza da sanya suturar zubar da mutunci da suke yi, a cikin makarantun da suke karatu, wanda hakan ke jefa su cikin mummunan zargi, rashin tsaro, da faɗawa tarkon ɗalibai marasa mutunci da za su iya cutar da su.
Amma ina son a fahimta cewa, wannan rubutu ba yana nufin cewa duk wasu ɗalibai maza ko mata da ke karatu a manyan makarantun aasar nan lalatattu ba ne ko ’yan iska ba ne. Sai dai ana samun baragurbi a cikinsu, waɗanda ayyukan assha da suke yi yana shafar masu tarbiyya da mutuncin sa suke karatu tare. Don haka nake kira ga iyaye mu yi aiki da hankali, mu tashi tsaye don gyara tarbiyyar yaranmu masu karatu a makarantu na nesa da gida ko na kusa da gida.
Masu ƙarfin faɗa a ji su sa baki lallai gwamnati ta samar da wani tsari na inganta tsaro a cikin makarantu, samar da wadatattun ɗakunan kwanan ɗalibai a cikin makaranta, da kuma sa ido kan walwalar ɗalibai da mu’amalarsu ta yau da gobe. A daidai wannan lokaci ya kamata a jinjinawa wasu malamai da shugabannin makarantu da ke kafa tsauraran dokoki, da sa ido wajen ganin tarbiyyar ɗaliban da ke ƙarƙashin kulawarsu a makaranta sun yi abin da ya dace, kuma sun gama cikin kyakkyawan sakamako.
Dakta Jibrin Shu’aibu Adamu, na Sashin Nazarin Harsunan Nijeriya da ke Jami’ar Bayero da ke Kano ya ba da wasu shawarwari shi ma game da yadda makarantu za su ƙara inganta yadda suke sa ido kan tarbiyyar ɗalibansu. Ya ce, babban abin da ya fi jan hankalinsa game da halayen rashin tarbiyya da wasu ɗalibai ke nunawa sun haɗa da sanya suturar zubar da mutunci da wasu ke sanyawa, tsakanin maza da mata. Duk kuwa da cewa akan kafa Kwamitoci masu yaqi da shigar banza a makarantu.
A cewarsa, lallai ne malamai su riqa kulawa sosai da ɗalibai masu shigar da ba ta dace ba a aji, kuma da zarar sun gansu, su kore su a ajin. Sannan masu tsaron makaranta, wato security su riƙa sa ido tun daga ƙofar shiga makaranta, suna dakatar da masu shigar banza zuwa shiga cikin harabar makaranta.
Wani abu da ya burge shi a irin wannan tsarin na dakatar da ɗalibai masu shigar banza zuwa cikin makarantu shi ne wani al’amari da ya faru a kan idonsa a Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano inda wani matashi ya nemi shiga da wando mai tsaga-tsaga a gwiwa, sai jam’in da ke tsaron ƙofar ya ce masa ba zai shiga ba. Sai da matashin ya nuna cewa shi ba ɗalibinsu ba ne takarda ya kai, da kyar aka bar shi ya kai saƙon.
Wannan rubutu nasiha ce da hannunka mai sanda ga iyaye da sauran masu faɗa a ji a harkar gudanar da makarantu, lallai a samar da tsari mai kyau na gyaran tarbiyya da sauya tunanin kangararrun ɗalibai. Sannan sauran nutsattsun da ke karatu cikin natsuwa da biyayya a samar musu da ingantaccen tsaro da kariya ga duk wani ƙalubale da za su iya fuskanta, wanda zai iya zama musu barazana ga karatunsu, mutuncinsu da rayuwarsu bakiɗaya.
