Nijeriya na kashe wa duk mutum ɗaya Dala 10 a fannin lafiya kullum – Ministan Lafiya

Spread the love
  • Za a saka wa ƙasashen da ke kwashe likitocin Nijeriya haraji, inji shi

Daga WAKILINMU

Nijeriya na kashe wa kowane mutum ɗaya Dala 10 a duk ranar duniya ta fannin kiwon lafiya da inganta rayuwa.

Ministan Lafiya na ƙasar, Farfesa Muhammed Ali Pate, shi ne ya bayyana haka a wani shiri da BBC Hausa ke yi lokaci bayan lokaci mai suna ‘A Faɗa A Cika’ da aka gudanar ranar Laraba a Abuja, lokacin da yake amsa tambayoyi game da abinda ya shafi ɓangaren lafiya, da suka shafi matsaloli, ƙalubale da kuma yadda za a magancesu.

Ali Pate ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ita kaɗai tana bada kaso 70 na kuɗaɗen da ake kashewa a fannin kiwon lafiya.

Yayin da aka tambaye shi wace hanya za a bi domin magance guduwar da likitoci ke yi daga ƙasar nan zuwa wasu ƙasashen domin qarancin albashi a wani ɓangaren ma albashin yakan gagari Kundila.

Ministan ya ce akwai matsaloli da dama da suke addabar fannin lafiya da ya kamata su likitocin su yi masa duba na tsanaki.

“Abin da ya dace su likitoci su fara dubawa shi ne, na farko dai ko da mutum ba a makarantar gwamnati ya yi karatu ba to babu makawa gwamnati ta taka rawa a al’amarin da ya shafi iliminsa ta wata fuskar, don haka kamata ya yi su fara duba kishin ƙasar kafin su yi tunanin barin ƙasar saboda rashin albashi. Nijeriya ƙasarmu ce kuma babu wanda zai zo ya gyara mana in ba mu ba.

“Na biyu kuma, su tuna cewa akwa jami’an da suka sadaukar rayuwarsu domin kare rayukan ‘yan Nijeriya kuma ake biyansu kudin da bai na su yawa ba, misali sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro, kuma aikinsu ya fi na likiton wahala, ka ga wannan ba wani abu ne ya illa kishin ƙasa, domin albashin nasu ba wani yawa ne da shi ba, wannan kishin ƙasa ne.

Don haka ya kamata qasashen da suke ɗauke mana likitoci su fara biyanmu kuɗaɗe da muka kashe wajen basu ilimi domin mu samu sukunin maye gurbin waɗancan da suka ɗauke mana,” inji shi.

Ya ce cututtuka sun ƙaru kuma kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa wajen kula da lafiyar jama’a ma sun ƙaru, domin magungunan ba a nan Nijeriya muke yi ba, zuwa muke mu sayo daga wasu ƙasashe mu shigo da su, kuma yanzu kowa yasan yadda farashin Dala yake, don haka dole sai gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi da kuma jama’a sun taimaka wa gwamnatin tarayya, an yi bincike kan mutum 2,500 ta hakan muke ƙoƙarin bunqƙasa lafiya a matakin farko yadda za mu gina asibitoci na sha-ka-tafi a kowace mazaɓa.

“Kuma abin da ya kamata mutane su sani shi ne, gwamnatin tarayya ita kaɗai tana ba da kaso 70 na kuɗaɗen da ake bayarwa a fannin kula da lafiya. A kullum Dala 10 ake kashewa ga lafiyar ɗan Nijeriya, Ingila Fam 5,000, Amurka Dala 14,000. Mutum miliyan 1.7 ne marasa lafiya ke cin gajiyar wannan tallafi,” inji shi.

Da aka tambaya shi kan Inshorar lafiya kuwa, sai ya ce, tun a 1974 Nijeriya ta fara shirin Inshorar lafiya. Bincike ya nuna kaso 10 ne daga cikin ‘yan Nijeriya suke da Inshorar lafiya, don haka a yanzu shugaban ƙasa ya rattaba hannu a kan tilas a shigar da kowane ɗan Nijeriya cikin Inshorar lafiya.

Da aka zo batun masu ciwon ƙoda kuwa, shwara ya bayar inda ya ce daga kan masu ciwon ƙoda, Siga, HIV da hawan jini, kai har ma da waxanda basu kamu da waxannan cututtuka ba, ya kamata su riƙa zuwa asibiti ana duba lafiyarsu a gani mutum yana da su ko bai da su. A taƙaice dai a halin yanzu abin da muka sa a gaba shi ne bunƙasa tattalin arziƙi da inganta lafiya.

Ɓangaren cutar HIV kuwa, cewa ya yi “Nijeriya ta farga daga sakacin da aka yi baya, tsarin da muke kai shi ne, gwamnatoci a dukkan matakai da ƙungiyoyi da sauran mutane sai sun taimaka wa gwamnati domin yaƙi wajen magance matsalar. Idan aka hannu domin magance matsalar babu shakka za a samu nasara fiye da yadda cutar ke ci gaba da yaɗuwa.

Kuma lallai ne kamar yadda na faɗa mutane su tashi tsaye wajen ganin sun je wurin likita domin duba lafiyarsu don su samu tabbaci a lafiyarsu domin haka ne zai sa mutum ya samu nutsuwa a fannin lafiyarsa da ta iyalinsa, wannan shi ne abin da ya dace.

By Editor