APC zaɓe ko ƙwace?

Spread the love

Ga dukkan alamu jam’iyya mai mulki APC tana daf da kwace duk kujerun gwamnonin arewa. Jihar Kano ce ta farko wajen yiwuwar ta zamo ta APC amma idan Kotun Ƙoli ta tabbatar da hakan.

Sai jihar zamfara wacce ga alamu sai an sake zaɓe a wasu yankuna a tsakani gwamnan PDP mai karagar mulki da kuma tsohon gwamna na APC wanda minista ne a yanzu. Jihar Filato ma a cen kotu ta kwace kujera ta gwamnan PDP ta mayar ga gwamnan APC wanda su kai takara. Amma mu kula da kyau?

Dukkanin inda a ke ƙwace kujeru na gwamnoni ko na ’yan majalissu ba duka ne na APC ba ai a jihar Bauchi an kori ƙarar APC an tabbatar ma PDP haka a jihar Adamawa duk da dai ba a ida zaman kotunan ba don haka yan siyasa ku dunga shirya gaskiya wajen gabatar da takardu na gaskiya da kuma kauce ma yin aringizo na kuriu domin ita kotu da hujja ta ke aiki.

Jam’iyyar APC ba kwace ta ke yi ba. Kotu ke ruguje maguɗi da cuwa-cuwa.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa. 07066434519/08080140820.

By Editor