*”Akwai shifcin gizo da aringizo cikinsa”
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babbar Jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, ta roqi Majalisar Dokoki ta Ƙasar, wato Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai da cewa, kada su amince da kasafin kuɗi na 2024, domin cike ya ke maƙil da aringizo, almara da rainin hankali ga talakawa.
Sakataren PDP na Ƙasa, Debo Ologunagba, ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Alhamis, kwan ɗaya bayan Shugaba Bola Tinubu ya kammala gabatar da kasafin a gaban gamayyar zauren Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya a Abuja a ranar Laraba.
Kasafin na Naira Tiriliyan 27.5 dai PDP ta ce akwai rufa-rufa damƙam a cikinsa. Don haka ta roƙi majalisa ta yi amfani da Kundin Dokokin Nijeriya Sashe na 80, 81 da 82 na 1999 su watsar da kasafin.
PDP ta ce, maimakon majalisa ta yi amfani da kasafin mai cike da shifcin-gizo, ta yi watsi da shi ta hanyar bijiro da kasafin da zai amfana wa talaka da tattalin arzikin ƙasar nan baki ɗaya.” Haka Ologunagba ya bayyana.
“Saboda a cikin kasafin akwai rufa-rufa, shifcin-gizo, lissafin-dokin-Rano da kuma uwa-uba aringizon maimaita wasu ayyuka da dama sau biyu.”
Ya ce batutuwa da dama da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bijiro da su a cikin kasafin na 2024, ba za a iya aiwatar da su ba, saboda an ƙirƙiro su ne a kan hasashen da aka yi wa kirdado bisa ta hanyar yin amfani da alƙaluman ƙididdigar lissafin dokin Rano.”
Ya ce, kasafin cike ya ke da buƙatun kashe maƙudan kuɗaɗe wajen samar da kayan alatun jin daɗin more rayuwar shugaban ƙasa, wanda tun tuni ya ke mafarkin samu, sai yanzu dama ta samu.
Ya ce, ba daidai ba ne kasafi ya ta’allaƙa wajen kashe biliyoyin kuɗaɗen da za a ciwo bashi ana narka wa wajen holewar shugaba, shi kuma talaka an bar shi cikin gaganiya da tsadar rayuwar da shugaban ya jefa shi a ciki.
