Super Eagles ta faɗo mataki na 42 a teburin FIFA

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Super Eagles ta Nijeriya ta yi ƙasa zuwa mataki na 42 a jerin waɗanda ke kan gaba a ƙwallon aafa a duniya, kamar yadda FIFA ta sanar.

A jadawalin da FIFA ta fitar ranar Alhamis, Nijeriya ta ɓarar da maki 16.04, wadda ta haxa 1474.44, wadda ta ke da maki 1490.48 a cikin Oktoba.


Sai dai wannan koma bayan bai shafi matakin Super Eagles a nahiyar Afirka ba, har yanzu tana nan a matsayi na shida.

Biye da Moroko da Senegal da Tunisia da Algeria da kuma Masar a jerin waɗanda ke kan gaba a taka leda a Afirka.

Wannan makin da Nijeriya ta barar ya biyo bayan tashi 1-1 da Lesotho da kuma Zimbabwe shima 1-1 a wasannin neman shiga gasar kofin duniya.

Har yanzu Argentina ce ta ɗaya a duniya, sai Faransa ta biyu da kuma Ingila ta uku a sahun farko-farko, yayin da Belgium ta yi sama zuwa mataki na huɗu.

Brazil ta ci karo da koma baya, wadda ta koma ta biyar ta rasa gurbi biyu, hakan ya biyo bayan doke ta da Colombia da Argentina suka yi a wasannin shiga gasar kofin duniya yankin Kudancin Amurka.