Daga BASHIR ISAH
Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC), ta amince da cire jami’o’i da sauran manyan makarantun ƙasar nan daga tsarin biyan albashi na bai-ɗaya, IPPIS.
Da wannan, yanzu makarantun da lamarin ya shafa su da kansu za su riƙa kula da biyan albashin ma’aikatansu.
Ministan Ilimi, Farfesa Mamman Tahir, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala zaman majalisar a ranar Laraba a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ya ce gwamnati ta yanke shawarar cire manyan makarantu daga tsarin biyan albashi ns IPPIS ɗin ne saboda damuwa da son ganin harkokin makarantun suna gudana yadda ya kamata da kuma kyakkyawan tattalinsu.
