Na yi ritaya daga siyasa, cewar Abdullahi Adamu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce ya yanke shawarar barin harkokin siyasa, inda ya ce ya lura cewa siyasa ta fita daga ran sa.

Adamu ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da wani littafi mai suna ‘Progressive Governance, Showcasing The Achievements of Governor Abdullahi Sule of Nasarawa State 2019–2023’ wanda Abdullahi Tanimu ya wallafa.

Tsohon shugaban jam’iyyar APC ɗin, wanda shi ne gwamnan farar hula na farko a jihar, kuma ya yi mulki a tsakanin 1999 zuwa 2007, yayin da yake magana kan littafin mai shafuka 230, ya yaba wa marubucin bisa ƙoƙarin da ya yi na bayyana nasarorin da gwamnan ya samu.

Ya ce gwamnan ya ɗora a kan nasarorin da waɗanda ga gada suka samar tare da inganta su, yayin da ya shawarci masu ruwa da tsaki da al’ummar jihar da su ci gaba da yi wa gwamna da ‘yan majalisarsa addu’a don ba su damar kai jihar ga wani matsayi mai girma.

Adamu, wanda ya ƙaddamar da kwafi 20 na littafin a kan Naira miliyan 1, ya bayyana cewa, “Ni ba ma ritaya kaɗai na yi ba, na ma fita daga harkokin siyasa.

Na fara jin cewa siyasa ta fara fita daga rai na kuma na daina ma maganar ta.

“Don haka ku yafe min, ba zan yi wata magana ta siyasa da ta wuce neman qarin goyon baya ga gwamnan jihar ba.

“Yana buƙatar dukkan addu’o’inku da fatan alheri don samun nasara.”

By Editor