Daga BASHIR ISAH
Wasu mata masu zanga-zanga sun kona gidan Dagacin Bokkos, Michal Monday Adanchi, da ke yankin Karamar Hukumar a Jihar Filato.
MAHAJA ta kalato cewar, lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Alhamis da misalin karfe 12:30am.
Majiyarmu ta ce matan sun kona gidan basaraken ne biyo bayan tsare wasu ‘yan kauyen da aka yi bisa zarginsu da hannu cikin kashe-kashen da ya auku a yankin a baya-bayan nan.
A cewar majiyar, “Lamarin ya faro a ofishin ‘yansanda inda matan suka nuna fushinsu dangane da tsare wasu ‘yan uwansu da aka yi.
“Bayan da suka baro ofishin ‘yansanda ne sai suka zarce zuwa gidan Dagacin, tare da zanga-zangar nuna fushinsu kan cewa lallai an saye shi ne.
“Jim kadan bayan isa gidan basaraken ne sai suka banka wa gidan wuta,” in ji majiyar.
Bayanai sun ce, sojoji sun hallara wurin inda suka tarwatsa masu zanga-zangar.
Da aka nemi jin ta bakinsa, Kakakin ‘yansandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya ce a ba shi lokaci ya tuntubi DPO don samun karin haske, in ya so daga bisani zai yi jawabi.
