Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekara biyar kan Farouk Lawan

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin daurin shekara biyar da a baya kotu yanke kan a kan tsohon dan Majalisar Wakilai, Farouk Lawan, bayan da ta kama shi da laifin karbar cin hancin $500,000 daga hannun Femi Otedola.

Lawan ya daukaka kara zuwa Kotun Koli ne inda ya nemi kotun ta yi watsi da hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke a kansa ran 24 ga Fabrairun 2022 wanda ta daure shi shekara biyar a gidan yari.

Sai dai, hukuncin da Mai Shari’a John Okoro ya rubuta wanda Mai Shari’a Tijjani Abubakar karanta, kotun ta yanke cewa karar da Lawan ya daukaka ba ta da hurumin da za a saurare ta don haka ta yi watsi da karar.

Baki daya alkalan Kotun su biyar sun yi ittifaki kan cewa, Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta yi daidai a hukuncin da ta yanke na ta daure Lawan shekara biyar a kurkuku bayan kama shi da laifin karbar cin hanci.

A shekarar 2021 aka yanke wa Lawan hukunci tare da tura shi kurkuku bisa karbar cin hanci na $500,000 daga hannun hamsahakin dan kasuwar nan, wato Femi Otedola.

By Editor