Maida hukumomin gwamnatin Legas: Soki-burutsu ’yan siyasar Arewa ke yi, inji Sanusi

Spread the love

*’Yan Nijeriya na cece-kuce kan dauke canja mazaunin CBN da FAAN

Daga SANI AHMAD GIWA da MAHDI M MUHAMMAD

Mai Martaba Sarkin Kano na 14, Malam Muhammadu Sanusi II, ya ce, “surutu” da soki-burutsu kawai ’yan siyasar Arewa ke yi dangane da shirin Babban Bankin Nijeriya (CBN) na dauke ragamar gudanarwa na wasu sassan bankin daga Babban Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja zuwa birnin Legas, wanda shi ne tsohon hedikwatar kasar.

Sarki Sanusi ya bukaci hukumomin da lamarin ya shafa da su yi watsi da surutan da ‘yan siyasar Arewa ke yi kan batun, saboda a cewarsa, Abuja a matsayin Babban Birnin Tarayya ba matsalar Arewa ba ne.

Idan dai za a iya tunawa, tun bayan da CBN ya bada sanarwar shirinsa na dauke wasu muhimman sassan CBN daga Abuja zuwa Legas, aka yi ta ce-ce-ku-ce a sassan kasa.

Lamarin da wasu ‘yan siyasa musamman daga Arewacin Nijeriya, suke ganin hakan ba zai sabu ba,  tare da gargadin irin sakamakon da daukar wannan mataki zai haifar.

Jaridar Intelregion ta raiwato cewa, a wata sanarwa da ya fitar, Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi, ya nuna goyon bayansa kan kudurin CBN din, yana mai cewa hakan ya yi ma’ana.

Sanusi ya yi kira ga Gwamnan CBN Yemi Cardoso, da ya yi la’akari da mata masu ‘ya’ya da masu matsalar rashin lafiya yayin da ya tashi dauke vangarorin CBN zuwa Legas.

Sai dai a karshe Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce ba shi da niyyar dauke babban birnin tarayyar kasar daga Abuja zuwa Legas.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, ya ce masu jita-jita ne ke yada maganar domin jan hankalin al’umma gare su.

“An soma watsa wannan jita-jitar a lokacin yakin neman zabe a bara inda ‘yan adawa ke neman duk wasu hanyoyi na dakile shi.”

Wannan na zuwa ne bayan matakin da Gwamnatin Tarayyar ta dauka na mayar da wasu bangarori na Babban Bankin Nijeriya CBN da kuma Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama FAAN daga Abuja zuwa Legas.

Lamarin da ya janyo korafi da kiraye-kiraye daga wasu kungiyoyi na wasu vangarorin kasar, inda suka yi zargin cewa tamkar wani mataki ne aiwatar da wata manufa ta daban.

Onanuga ya ce matakin mayar da wani sashi na FAAN bai kamata ya ja hankalin mutane da yawa ba saboda Jihar Legas ita ce cibiyar kasuwanci kuma cibiyar sufurin jiragen sama a Nijeriya, saboda haka ya ce har yanzu FAAN za ta ci gaba da kasancewa a Abuja.

Ya kuma bayar da misali kan cewa akwai ma’aikatun Gwamnatin Tarayya da hedikwatarsu ba a Abuja take ba, wadanda suka hada da NIMASA da NPA ke Legas haka kuma akwai NIWA da ke Lokoja.

“Akwai ma’aikatu da yawa da ba a Abuja suke ba dangane da aikinsu kamar NIMASA da take Legas. Haka kuma NPA da kuma Hukumar Kula da Sufurin Ruwa (NIWA) da ke Lokoja.”

Sanarwar dai ta kara da cewa bai kamata a siyasantar da lamurran gwamnati ba.

Tun bayan da Babban Bankin Nijeriya CBN ya sanar da shirinsa na dauke wasu muhimman sassan bankin daga Abuja zuwa Legas, kazalika ita ma Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama FAAN ta bada sanarwarta, aka yi ta ce-ce-ku-ce a sassan kasar, inda ‘yan siyasar Arewa suka ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da dambarwar dauke wadannan muhimman wurare daga Babban Birnin Tarayya zuwa Legas, mahaifar Shugaba Tinubu. Ga dai abinda ‘yan siyasar ke fada:

Ba za mu bari a zalunci Arewa ba, inji Ndume:

Mai tsawatarwa a Majalisar Dattawan kasar Sanata Mohammed Ali Ndume ya shaida wa BBC cewa matakin da gwamnatin ta dauka ya savawa kundin tsarin mulkin kasar wanda ya tanadar cewa Abuja ce birnin tarayya kuma a nan ya kamata a ce duk wata hedikwatar ma’aikatar gwamnati take, kuma samun akasin haka zai iya cutar da yankin Arewacin kasar.

Daga cikin dalilan da gwamnatin ta bayar na daukar wannan matakin shi ne rage cunkoso a ma’aikatun gwamnati da ke Abuja, wanda ta ce yana kawo nakasu wajen yadda ake gudanar da ayyuka a ma’aikatun.

 Amma Sanata Ndume ya ce hakan ba dalili ba ne, “A duk Nijeriya babu inda ya kai Legas cunkoso, idan ana gudun cunkoso ne, a cikin Abuja akwai fili ko ta ina, a cikin hukumomin gwamnati wadanda aka rage su ma suna da hedikwata da za a iya amfani da su idan har cunkoso ake son a ragewa,” inji shi.

Ya kara da cewa dole ne gwamnati ta yi adalci a duk wani mataki da za ta dauka saboda ka da kowanne bngare su ga kamar ana neman a muzguna masu.

Sanatan ya ce, “Ina da tabbacin cewa kundin tsarin mulki bai yarda a zartar da wani matakin gwamnati da zai cutar da wani vangare ba, kuma mu ‘yan majalisa na Arewa ba za mu zauna muna gani a cutar da vangaren da muke wakilta ba, idan mun yi haka yana nufin ba mu yi aikinmu yadda ya kamata ba. Dole ne a yi mana adalci kuma adalcin nan shi ne a bar hukumomin nan a inda suke a hedikwtar kasa, ba mu amince a zalunce mu ko ta wani hanya ba kuma mu ma ba za mu zalunci kowa ba.”

Wannan dai shi ne karo na biyu da wata kungiyar Arewa za ta yi Allah-wadai da sauya wa hukumomin gwamnatin tarayyan biyu matsuguni.

A baya dai kungiyar tuntuva ta Arewa (ACF) ta soki wannan lamarin, inda ta ce wannan matakin zai haifar da rashin cigaban yankin Arewacin kasar.

Game da batun kasafin kudin 2024 da wasu ke ganin kamar an fifita wani bangaren kasar, Sanata Ndume ya yi bayanin cewa ‘yan majalisa za su yi nazarin kasafin kudin da nufin gano yadda aka kasafta kudade tsakanin bangarorin kasar domin su tabbatar da cewa an yi adalci.

Ya ce: ‘Idan mun duba mun ga an yi rashin adalci za mu duba hakkin da ya rataya a wuyanmu na wakiltar jama’a, kuma za mu tabbatar cewa ba a cuce mu ba kuma mu ma ba mu cuci kowa ba.”

Ko gwamnatin tarayya ta canja shawara ko kuma mu hadu a kotu – Sanatocin Arewa

Sanatocin Arewacin Nijeriya sun bayyana cewa mayar da ofisoshin CBN da FAAN zuwa legas wata makarkashiya ce ta gurgunta Arewa. 

Kungiyar Sanatocin Arewa NSF ita ta bayyana haka. Hakazalika kungiyar kuma ta yi Allah-wadai da batun dai na mayar da wasu sassan Babban Bankin Nijeriya da hedikwatar hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa FAAN daga Abuja zuwa jihar Legas.

Sanatocin sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta canja shawara tun da wuri ko kuma su hadu a kotu.

Sanata Abdurrahaman Kawu Sumaila, mai magana da yawun Kungiyar NSF ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

Sanata Kawu, dan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya bayyana cewa ‘yan Arewa ba su gamsu da mayar da hukumomin gwamnatin tarayya biyu zuwa Legas ba.

Ya ce sanatocin Arewa sun fara tattaunawa da takwarorinsu na sauran shiyyoyin domin ganin an mayar da sassan da aka mayar da su a hukumomin tarayya biyu zuwa Abuja.

Baya ga sanatocin qungiyar dattawan Arewa sun nuna vacin ransu a baya cewa yin haka hanya ce kawai na gurgunta yankin Arewa.

Kungiyar ta kuma ce a matsayinta na mai wakiltar jama’ar yankin a matakin kasa, ya zama wajibi ta yi duk mai yiwuwa wajen magance matsalolin da ake fama da su na karkata da wasu kudade a cikin kasafin kudin 2024, da mayar da wasu hukumomin tarayya daga Abuja zuwa Legas.

Matasan Arewa sun yi watsi da matakin komawar sassan CBN Legas:

A farkon makon nan ne hadaddiyar Kungiyar Matasan Arewa, wacce ta hada kungiyoyi 16 daga sassan jihohin Arewacin kasar nan suka gudanar da wani taron manema labarai a Kaduna domin su nuna rashin amincewar su da take-taken gwamnatin Tinubu na mayar da wasu muhimman sassan babban bankin Nijeriya daga Abuja zuwa Legas, wanda suka ce ya saba ma ka’idar samar da Abuja. 

Taron, wanda ya gudana a dakin taro na gidan Sardauna da ke Arewa House ranar Litini, Shugaban tawagar kungiyoyin, Malam Murtala Abubakar ne ya jagoranta, inda ya bayyana cewa “A yau mun hada ku a nan ne domin mu nuna adawar mu da damuwar mu kan shawarar mayar da wasu muhimman sassa guda biyar na Babban Bankin Nijeriya (CBN) daga Abuja zuwa Legas.

“Da kuma batun mayar da hedikwatar hukumar kula da filayen jiragen sama ta tarayya (FAAN) da ma’aikatar sufurin jiragen sama ta tarayya ta yi daga Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya zuwa Legas.”

Daga nan sai Malam Murtala ya ce, “Mu, kungiyoyin matasan Arewacin Nijeriya, muna wakiltar murya da muradun miliyoyin matasa daga yankin Arewacin kasar nan ne, wadanda wannan shawarar ta shafa.

Mun yi imanin cewa ba kawai ayyukan rashin gaskiya ba ne, har ma da illa ga ci gaban tattalin arziki, zamantakewa da siyasa na yankin Arewa da ma kasar baki daya.

Ya ce, suna wannan magana ce saboda zaman su al’umma masu da’awar hadin kan ’yan kasa, da zaman lafiya, tare da ci gaban wannan kasa mai albarka, inda suka ce tun farko ma dai, babban bankin ba shi da hurumin daukar wannan mataki, musamman bisa la’akari da dokar da ta kafa Babban birnin tarayyar.

Da ya ke tsokaci game da sassan masu muhimmanci da Babban bankin zai dauke zuwa Legas kuwa, Malam Murtala cewa ya yi, “Muna tambayar dalilan da ya sa Babban Bankin kasa daukar wannan mataki a kan muhimman sassan sa biyar, wadanda suka hada da sashen Kula da Harkokin Bankuna; Sashen Kula da Sauran Cibiyoyin Hada-hadar Kudi; Sashen Kula da Bukatun Masu hulda da Bankuna; Sashen Tsarin Sarrafa Biyan Kudade da Sashen Dokokin Hada-hadar Kudi.”

Babban Bankin ya kawo hujjar daukar wannan mataki na komawa Legas, inda ya ce ya dauki wannan tsari ne domin rage cunkoso a babban ofishin sa da ke Abuja, wanda aka gina domin ma’aikata 3,000, amma yanzu yana da 4,000.

To, amma sai dai Matasan sun yi nuni da cewa wannan dalili ba shi da karfi, domin babban bankin ai zai iya fada ofishin nasa a Abuja cikin sauki, ko kuma ya raba ma’aikatan nasa zuwa wasu yankuna, maimakon ya tattara su a Legas.

Hadakar matasan Arewar suka ce, mayar da wadannan manyan sassa guda 5 zuwa Legas zai haifar da mummunar illa ga hada-hadar kudi, kwanciyar hankali da tsaron kasar nan, wanda hakan zai haifar da tazara tsakanin Babban Bankin kasa da gwamnatin tarayya mai Hedikwatar a Abuja, da kuma kawo cikas ga daidaito da sadarwa a tsakanin su.

“Haka kuma zai rage wa cibiyoyin hada-hadar kudi da kwastomomi na sauran yankunan kasar nan, musamman Arewa, wacce tuni ta ke fama da karancin cibiyoyin hada-hadar kudi.

Korafi da koken matasan Arewan, ba a Babban Bankin kadai ya tsaya ba, sun kuma yi tofin Allah-tsine ga Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Tarayya bisa matakin da ta dauka na mayar da Hedikwatar Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama na FAAN zuwa Legas, “Wanda hakan ya sava wa ka’idar da’a ta tarayya da ke cikin Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya,” inji matasan.

Suka ce, “Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama dai Hukuma ce mai kula da kuma gudanar da dukkan filayen tashi da saukar jiragen sama na kasar nan, ba wai na Legas kadai ba. Saboda haka, ta hanyar mayar da hedkwatarta zuwa Legas, FAAN na lalata tsarin tarayya na kasar nan da kuma tsarin wakilci na daidaito da shigar da dukkan jihohi da yankuna a harkokin mulki da gudanar da mulkin kasar.

“Hakan kuma zai haifar da mummunar illa ga tsaro da ingancin filayen jiragen sama a sauran sassan kasar nan, musamman Arewa, wadanda tuni ke fuskantar kalubale na rashin cikakken kulawa, da kashe masu kudi da rashin cikakken amfani da su.”

A karshe, matasan sun jawo hankalin gwamnati da cewa, “Don haka muna bukatar gwamnatin tarayya ta janye wadannan matakan da Babban Bankin kasa da Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama suka dauka cikin gaggawa, sannan ta dawo da martabar Abuja, Babban Birnin Tarayya.

An zabi Abuja ne a matsayin babban birnin kasar nan don zamowar ta a tsaka-tsaki ga jinsunan da yankunan kasar. Har ila yau, Abuja tana taimaka wa wajen daidaitawa ga yankuna da sassa daban-daban na kasar nan.

“Saboda haka in gwamnati ta mayar da manyan sassa 5 na Babban Bankin kasa da hedikwatar Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama zuwa Legas, to ba wai kawai rashin mutunta zabi da hangen nesa na wadanda suka kafa Abuja ba ne, har ma da haifar da kyama a tsakanin al’ummar yankin Arewa da sauran yankuna, wadanda ba su da wakilci a Legas. 

Kungiyoyin da suka hadu a wannan taro, sun hada da ‘Arewa Defense League, Association of Northern Nigerian Students, Arewa Youth for Development and National Unity, Arewa Young Women’s Rights Advocate Council, Northern Youth in Defense of Democracy, Arewa Radio and Television Commentators, Northern Youth Democratic Agenda Da kuma The Time is Now, the Time is Ours Association.’

Sauran sun hada da ‘Arewa Youth Advocate for Peace and Unity Initiative, Northeast Youth Artisans Association, Bauchi State Citizens Action for Chang, Youth Initiative for Good Governance, Coalition of Tiv Youth Organization, Matasan Arewa Ina Mafita Development Association, Toro Youth Circle da Northern Youth Coalition Forum.

By Editor