’Yan sanda sun ƙi karɓar cin hancin Miliyan N8 daga ’yan bindiga a Taraba

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba ta kama wasu mutane 13 da ake zargin ’yan fashi ne da masu garkuwa da mutane da suka addabi mazauna qananan hukumomin Jalingo, Yorro, Lau, da Zing na jihar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Joseph Eribo ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin tare da baje kolin su a hedikwatar ’yan sanda da ke Jalingo, babban birnin jihar a ranar Laraba.

Kamen dai ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da jama’a suka yi kan munanan ayyukan ‘yan ta’addar wanda a cewar ‘yan sandan ya ɗauki wani salo mai ban tsoro.

A cewar rundunar ’yan sandan, ’yan bindigar na amfani da tsaunukan da ke kusa da su a matsayin maɓoyar garkuwa, kuma duk wani yunkuri na ceto waɗanda abin ya shafa ko kai wa ‘yan fashin hari kan haifar da barna, don haka ta yanke shawarar tura dukkan karfinta na aiki don tunkarar wannan lamari da ya kunno kai.

Bayan haɗin gwiwar ’yan sanda da sauran jami’an tsaro da kwararrun mafarauta, an cafke 13 daga cikin ‘yan fashin a sassa daban-daban na jihar. An yi watsi da kudin fansa sama da Naira Miliyan 8 a matsayin cin hanci, sannan an kwato bindigu kirar AK-47 guda biyar da alburusai biyar tare da ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su.

An kuma kama wasu barayin wutar lantarki guda uku da laifin kutsawa tare da lalata taransifoma na hedikwatar ‘yan sanda tare da lalata kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Yola (YEDC) a karamar hukumar Lau ta jihar.

’Yan fashin da masu garkuwa da mutane a yayin da ake yi musu tambayoyi sun ce yawanci suna hada kai da masu lalata wutar lantarki wajen lalata na’urar taransifoma da ke ba su damar yin garkuwa da mutane cikin duhu.

Rundunar ’yan sandan ta kuma kama wani da ake zargin dan fashi da makami ne da ya sace mota a hannun wanda abin ya faru amma daga baya ‘yan sandan suka gano shi.

Wasu daga cikin ’yan fashin da ake zargin su da hannu wajen yin garkuwa da wani basaraken gargajiya, Fasto, da Limami da kuma wani mai garkuwa da mutane da ya karbi kudin fansa sama da Naira Miliyan 8 da dai sauransu sun amsa laifin su.

Rundunar ‘yan sandan ta ce za a gurfanar da duk waɗanda ake zargin a gaban kuliya kamar yadda dokar hana garkuwa da mutane ta jihar ta tanada kuma za ta tabbatar da an yi adalci.

A yayin da yake nanata cewa rundunar za ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin mazauna yankin, kwamishinan ‘yan sandan ya yaba wa Gwamnan Jihar, Agbu Kefas, bisa ga irin goyon bayan da yake bai wa hukumomin tsaro, domin ganin an samar da zaman lafiya da haɓakar tattalin arziki.

By Editor