Tinubu ya isa Abuja bayan kammala ziyara a Faransa

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya isa birnin tarayya, Abuja, bayan kammala ziyara a kasar Faransa domin gudanar da harkokinsa.

Tinubu ya sauka filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ne da misalin karfe 8:50 na dare inda ya samu tarba daga tawagar gwamnati karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume.

Haka nan, tawagar takunshi manyan jami’ai irin su Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila; Ministan Abuja, Nyesom Wike da sauransu.

Tun a ranar Laraba ta makon jiya Tinubu ya bar Nijeriya zuwa Faransa, kuma wannan ita ce ziyararsa ta biyu a kasar tun bayan da ya zama Shugaban Kasa a watan Mayun 2023.

By Editor