Shugaban UBEC ya buƙaci a riƙa koyarwa da harshen uwa a makarantu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

UBEC ta gano rashin halin ko-in-kula da ake saka wa wajen aiwatar da manufofin harshe kan amfani da harshen uwa a makarantu a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da ke kawo cikas ga ci gaban muradun ƙarni masu ɗorewa, SDGs, a Nijeriya.

Sakataren zartarwa na hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta ƙasa ,UBEC, Dr Hamid Bobboyi ne ya bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja a ranar Litinin.

Taron na masu ruwa da tsaki na kwanaki biyu mai taken “Tattaunawa kan samar da dabaru na Karatu a Cikin Shirin UBE da Amfani da Harshen Uwa a Matakin Koyarwa Matsakaici,”

A cewar shugaban na UBEC, Nijeriya na fama da matsalar ilimi mai tsanani wanda ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa don magance matsalar.

Mista Bobboyi ya jaddada cewa, idan ba a gaggauta magance matsalar ilmantarwa ba, to hakan zai kawo cikas ga Nijeriya wajen cimma muradun ci gaba mai ɗorewa, SDGs.

Shugaban na UBEC ya bayar da misali da rahoton hukumar ƙididdiga ta ƙasa, da UNICEF kan ilimin boko a Nijeriya.

Rahoton, a cewarsa, ya ce kusan uku daga cikin huɗu na yara masu shekaru shida zuwa 14 a Nijeriya, ba su iya karanta rubutu ko aikin lissafi masu sauƙi ba.

Don haka ya yi kira da a tashi tsaye a samar da hanyoyin gyara cikin gaggawa.

By Editor