Daga BASHIR ISAH
Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamma Dauda Lawal ta fara biyan tsoffin ma’aikatan jihar bashin giraduti na Naira biliyan 13.4 da suke bin jihar.
Cikin sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Asabar, Kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya ce, gwamnati ta kafa kwamitin musamman da ke aikin tantance ma’aikatan da suka yi ritaya domin a biya su bashin giraduti da suke bi daga 2011 zuwa yau.
Idris ya kara da cewa, an tantance bashin giradutin na shekaru da tsoffin ma’aikatan ke bi, kuma tuni an fara biyan su tun daga ranar Alhamis da ta gabata.
Ya ce, “Gwamnatin jihar ta dauki matakin warware bashin giradutin da tsoffin ma’aikata ke bi da ya hada da giradutin mutuwa da na ritaya da kuma na kwantiragi.
“Gwamna Dauda Lawal ya kafa kwamitin da zai yi aikin tantance bayanan ma’aikaci domin a biya shi bashin giradutin da yake bi tun daga 2011.
“Bayan tantance tsoffin ma’aikatan, gwamnati ta gano bashin da ma’aikatan ke bi daga jiha zuwa kananan hukumomi ya kai Naira biliyan 13.4.”
Dauda ya kara da cewa, gwamnati za ta tabbatar da an biya daukacin tsoffin ma’aikatan hakkinsu ba tare da wata wahala ba.
Haka nan, ya ce “Gwamnatin Zamfara na kokarin cika alkawarin da ta daukar wa al’ummar jihar na ceto su da kuma sake gina jihar yadda ya kamata.”
