Yadda farashin kayan gwari ke hauhawa a Kebbi

Daga Jamil Gulma a Birnin Kebbi

Kayan gwari waɗansu kayan amfanin gona ne da mafi akasarinsu a kan sarrafa su ne a miya, waɗanda kuma ke da lokacin araha da kuma tsada da suka haɗa da tumatir, ataruhu, tattasai, albasa kabeji, sure ko yakuwa (taushe) alayyafo, guro, kabushi da dai sauransu.

Ana noma kayan gwari a yankunan arewacin Nijeriya, musamman a vangarorin da ke da fadama ko dausayi da qoramu, inda kusan kowacce jiha a Arewa akwai wani yanki da a ke iya samun su, sai dai kawai waɗansu yankunan sun fi waɗansu.

Tsadar kayan masarufi ba sabon abu ba ne a Nijeriya tun kafin wannan lokacin da mu ke ciki sai dai a yanzu abin ya zarce hankali, ya soma tsorata al’umma bisa ga ganin irin yadda farashin kayan abinci ke tsada kuma ba kuɗi a hannun mutane.

A ɓangaren masu sana’ar kayan miya kamar tumatir, ata, tattasai, albasa, kabeji, sure da alayyafo da dai sauransu da aka fi sani da kayan gwari da a ke yi wa kirari da ‘gwari ba kuɗi ba sai an saida’ su ma ba a bar su a baya ba, saboda a kullum suna ƙara tsada bisa ga dalilin ƙarancin kayan da makamantan hakan.

Wakilin Blueprint Manhaja ya zagaya babbar kasuwar gwari da ke garin Argungu a Jihar Kebbi, inda kamar nan ne cibiyar ’yan gwari daga garuruwan da ke kawo kaya daga waɗansu ƙananan hukumomi a Jihar Kebbi da kuma Sokoto.

Alhaji Bashiru, wanda shi ne shugaban ƙungiyar masu sayar da kayan miyar, kuma ya bayyanawa wakilinmu da cewa a halin yanzu albasa kaɗai ke sauƙi, saboda yanzu buhunta ana iya samun sa a Naira 26,000 zuwa da 28,000 savanin inda aka fito da an sayar da shi har Naira 100,000. Tumatir kuwa yanzu kwandonta Naira 26,000 zuwa 25,000 a inda aka fito bai wuce 15,000 zuwa 15,000 ba.

Tattasai kuma yanzu ya kai Naira 18,000 zuwa 20,000, savanin a baya da ake sayar da shi Naira 12,000 zuwa 13,000. Sanadiyyar ana ɗauko shi ne daga jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina har daga Zariya, saboda haka idan ka yi la’akari da tsadar kuɗin mota, dole ne ya yi tsada.

Tattasai da taruhu (ata) su ma ba a bar su a baya ba. A halin da a ke ciki sauran kayan dai sai dai a yi wa Allah godiya, saboda ana tafiya ne a faɗi a tashi.

Tsadar kayan gwari a wannan yankin yana da nasaba da ƙarancin manoman kayan, sannan kuma waɗanda ke noman su mafi yawancinsu masu ƙaramin ƙarfi ne kuma ba su tava samun wani tallafi daga gwamnatin Jihar Kebbi ko ta Tarayya ba ko a ƙunginyance ko kuma a ɗaiɗaiku.

Alhaji Basiru ya yi kira ga gwamnatin Jihar Kebbi da ta waiwayo masu wannan sana’ar ta noman kayan gwari da kuma masu sana’ar, don tallafa musu, saboda rashin samun tallafin yana daga cikin ummul’aba’sar tsadarsu, don manoman ba su iya noma kayan gwari da za ya wadatar da al’umma idan aka yi la’akari da yawan mabuƙata da ya rinjayi kayan da ake nomawa.

Malam Bashar, wani mai sayar da kayan miya a kasuwar tashar Nana da ke garin Argungu, ya bayyana cewa, shi ba ya zuwa ko’ina sai dai idan aka kawo ya kan sayi kwanduna na kayan miya shi kuma ya kasa a rumfarsa yana sayarwa. 

Ya ce, kamar yadda kowa ya sani abubuwa na rayuwa sun canza, ba kamar inda aka fito ba, saboda haka a lokacin da suke da sauƙi za a sayar da sauƙi, lokacin tsada kuma a sayar da tsada.

Malam Lauwal Muhammad, wani magidanci ya bayyana cewa, yana da mata biyu da ’ya’ya tara, saboda haka yanzu da safe mutum zai iya samun kayan da sauƙi, saboda akwai ’yan matan da da ke kawo kayan miya daga qauyuka, waɗanda ta hannunsu ka na samun kayan da sauƙi, amma idan ka bari rana ta yi, to sai dai ka saya a hannun masu sari, waɗanda su ma riba su ke nema.

Wani lokacin idan ya makara, sai dai ya sayi wanda ya soma lalacewa da a ke kira dameji sanadiyyar gidansa yana da yawa, idan ya ce zai sayi na ƙwarai, to zai sha tsada.

Ya ce, yana sayen kayan miya aƙalla na Naira 700, amma duk da haka sai matansa sun yi dabaru sannan zai isa.

Wata malama da ba ta so bayyana sunanta ba, wacce ke sana’ar abincin sayarwa, ta ce, ba ta da zaɓin da ya wuce ta sayi dameji, sai dai idan ta je gida ta kan tsaya ta gyara shi ta tsaftace shi, saboda idan ta sayi mai kyau sosai, za ta kashe kuɗi masu yawa ta yadda da wahala ta ci riba. Tana sayen kayan miya aƙalla na Naira 5,000 zuwa 7,000 a lokacin kakar kayan miya, amma idan kaka ta wuce sai na goma sha kuma wani abun duk da haka dai maleji ne ta ke yi.