Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Tawagar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya ta Super Eagles za ta haɗu da mai masaukin baƙi Ivory Coast a wasan ƙarshe na kofin nahiyar Afrika bayan nasararorin da ƙasashen biyu suka samu a wasanninsu na daren Laraba, wasan ƙarshen da zai gudana a ranar Lahadi 11 ga watan Fabarairu.
Nijeriya dai ta doke Afrika ta kudu ne da ƙwallaye 4 da 2 a bugun fenariti yayin wasan daf da ƙarshe ƙarƙashin gasar ta AFCON, nasarar da ta kawo ta wannan mataki na wasan ƙarshe wanda rabonta da kai wa tun a shekarar 2013 wanda kuma ta lashe kofin a wancan lokaci.
A vangare guda, Ivory Coast ta yi nasarar kaiwa wasan ƙarshen ne bayan doke jamhuriyyar Demokraɗiyyar Congo da ci ɗaya mai ban haushi.
Wannan nasara ta nuna yadda Super Eagles ta doke Bafana-Bafana sau 3 a jere yayin mabanbantan wasannin wannan gasa ta AFCON ciki har da dukan da ta yi mata a filin wasa na Legas cikin shekarar 2000.
Gabanin lashe kofinta a 2013 ko a shekarar 2000 Super Eagles ta kai wasan ƙarshe na AFCON lokacin da Nijeriya ta yi haɗin gwiwa da Ghana wajen ɗaukar nauyin gasar bayan da Zimbabwe ta gaza ɗauka.
A jumulla dai wasan ƙarshen da zai gudana ranar Lahadi tsakanin Njeriyar da Ivory Coast na nuna yadda Super Eagles za ta ɓarje gumi a wasan ƙarshe na gasar karo na 8.
Nijeriya dai ta haɗu da Ivory Coast a matakin rukuni inda ta doke ta da ƙwallaye 2.
