Daga BASHIR ISAH
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya samu amicewar Hukumar Shirya Jarrabawa ta WAEC kan sakin sakamakon daliban sakandaren jihar da hukumar ta rike.
WAEC ta rike sakamakon ne saboda bashin kudin jarrabawa sama da Naira biloyan 1.4 da take bin gwamnatin da ta gabata.
Kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a sanarwar da ya fitar cewar, a ranar Litinin Gwamna Lawal ya gana da shugabancin WAEC a ofishinsa da ke Abuja.
Ya kara da cewa, babbar jami’ar WAEC, Hajiya Binta Abdulkadir ce ya jagoranci tawagar hukumar yayin ganawar, yayin da sauran jami’an suka hada da Dr. Amos J. Dangut da sauransu.
A cewar sanarwa, “A matsayin bangare na kokarin da gwamnati mai ci ke yi wajen ingantawa da kuma magance matsalolin fannin ilimin jihar, Gwamna Dauda Lawal ya karbi bakuncin shugabannin hukumar WAEC a ofishinsa da ke Abuja.
“Gwamnan wanda ya samu rakiyar Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha, Malam Wadatau Madawaki, sun tattauna WAEC dangane da bashin da ake bin Jihar Zamfara na kudin jarrabawar da aka rubuta karkashin gwamnatin da ta gabata.
‘Yan bindiga sun kashe mutum 4 ciki har da ‘yan sanda, sun yi awon gaba da mutum 40 a Zamfara
Yadda manyan Arewa suka kassara cigaban yankin da al’ummarsa
“Rashin biyan kudin WAEC na shekaru ne ya sanya hukumar ta rike sakamakon jarrabawar daliban da lamarin ya shafa.”
Bayan kammala tattaunawar, a karshe hukumar ta amince ta saki sakamakon jarrabawar da ta rike kafin karshen wannan wata, kuma za ta bai wa daliban Zamfara zarafin rubuta jarrabawar WAEC na 2024.
