Yadda Sunday Igboho ya sake tako ƙafa Nijeriya bayan shekara uku

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Fiye da shekaru uku bayan ya tsere daga Nijeriya sakamakon samamen da aka kai masa a gidansa da ke Ibadan a ranar 1 ga Yuli, 2021, mai fafutukar kafa ƙasar Yarabawa, Mista Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, a ranar Laraba ya dawo Nijeriya.

Jaridar Blueprint Manhaja ta tattaro cewa, ya taso ne daga ƙasar Jamus, inda ya masu mafaka bayan wata kotu a Benion ta bada belinsa a bara.

Adeyemo, wanda ya kasance kan gaba a fafutukar tabbatar da ƙasar Yarabawa a ƙarƙashin inuwar Ilana Omo Oodua, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Banji Akintoye, da ƙyar ya samu sarara ya tsere daga Ibadan, da sanyin safiyar ranar 1 ga watan Yuli, 2021 a lokacin da wata tawagar haɗakar Jami’an Tsaron Farin Kaya (DSS) da Sojojin Nijeriya sun kai farmaki gidan sa da ke Soka, Ibadan, inda suka kashe mutum biyu.

Haka kuma sun kama magoya bayansa su 13, waɗanda aka gurfanar da su a gaban kotu, daga bisani wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Obiora Egwuatu ta bayar da belinsu.

Da yake tabbatar da zuwansa ta wayar tarho, Adeyemo ya ce, “Gaskiya na dawo ƙasar. Na dawo ranar Laraba da gangan don bikin binne mahaifiyata.

A cewarsa, “Dole ne in dawo gida in binne mahaifiyata. Ta rasu ne a shekarar da ta gabata, yau (Alhamis) ita ce ranar shiryata, gobe kuma za a yi jana’izarta a Igboho kafin mu wuce Ibadan domin bikin bayan da binnewa a ranar Asabar.

“Zan iya gaya muku cewa an kammala dukkan tsare-tsare don yiwa mahaifiyata jana’iza mai kyau sannan kuma manyan ’yan Nijeriya da manyan baƙi daga sassa daban-daban an ba su takardar izinin halartar jana’izar. Ina matuƙar godiya ga kowa da kowa bisa goyon bayanku da hadin kai a lokacin da nake fama da jarrabawa a Nijeriya da Jamhuriyar Benin,” inji Adeyemo.

By Editor