Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau
Ana zargin Dakarun Tsaron Al’ummar Jihar Zamfara (CPG) da yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin a jihar, Sheik Abubakar Hassan Mada yankan rago.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an na CPG sun yi dirar mikiya ne a gidan marigayin dake garin Mada ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Gusau a ranar Talata inda suka ɗauke shi zuwa wajen garin.
An ce jami’an sun tafi da shi domin yi masa tambayoyi dangane da matsalar rashin tsaro a yankin.
Wani mazaunin garin Mada da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa, jami’an CPG sun je har gidan Sheik Mada inda suka ɗauke shi zuwa wajen garin suka yi masa yankan rago.
“Da misalin ƙarfe 3:30 na rana kai tsaye suka zo wurinsa a lokacin yana koyar da ‘ya’yanmu, suka tafi da shi, bai wuce mintuna 20 ba, kwatsam sai muka ji cewar sun kashe shi ta hanyar yi masa yankan rago,” in ji shi.
A cewarsa, kimanin shekara ɗaya da ta gabata, Sheik Abubakar Hassan Mada ya shiga tsakani wajen ceto wasu masu sana’ar Okada su biyar daga hannun ‘yan banga waɗanda suka tare su tare da zargin su a matsayin ‘yan ta’adda a hanyarsu ta komawa gida daga wajen jihar, wanda hakan ya sa wani ɗan banga da aka fi sani da suna Maikarfi ya zargi Sheik Abubakar Hassan Mada da haɗa baki da ‘yan ta’adda tun a wancan lokacin.
“Wannan al’amari ya faru ne sama da shekara guda, kuma hatta hukumar binciken manyan laifuka ta rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta san da haka kuma bayan sakin waɗannan ‘yan Okada, ‘yan bangan ƙarƙashin jagorancin Maikarfi sun zargi Sheik Abubakar Hassan Mada da haɗa baki da ɓarayin daji.
“Maikarfi ya samu damar kasancewa ɗan ƙungiyar kare al’ummar Zamfara kuma muna tuhumarsa da kitsa kashe Sheik Mada.
“Muna kira ga gwamnatin jihar Zamfara da ta binciki lamarin tare da gurfanar da waɗanda suka kitsa kisan gillar da aka yi wa fitaccen malaminmu,” in ji majiyar.
Har ya zuwa lokacin haɗa rahoton, ƙoƙarin da aka yi don jin ta bakin Kwamandan CPG na jihar, Kanal Yandoto (rtd) ya ci tura.
