Babban ƙalubale a Nijeriya

Spread the love

Daga NAFI’U SALISU

Akwai abubuwa da dama waɗanda suke faruwa a ƙasar nan, waɗanda sune babban ƙalubalen da yake hana mu zama lafiya da kwanciyar hankali tare da ci gaban kanmu da kanmu. Daga lokacin da muka yi tunani mai kyau, kuma muka ɗaura ɗamarar gyarawa, to ko shakka babu al’amurranmu za su sauya..

Kafin mu yi kuka da hawaye ko babu hawaye, yana da kyau mu fara dubawa mu ga menene dalilin yin kukan namu? Domin kuwa komai da yake faruwa a rayuwa yana da dalili, babu wani abu da ke faruwa haka kawai ba tare da sila ba.

Ina so in yi babban sharhi a game da yadda rayuwarmu take gudana a matsayinmu na ‘yan Nijeriya, babbar ƙasa a nahiyar Afirka mai cike da arziki da albarkatun ƙarƙashin ƙasa da na tudu, waɗanda babu wata ƙasa a Afrika da ta mallake su. To amma duk ƙasar da take da arziki da albarkatun ƙasa a wannan nahiya tamu ta Afrika, dole akwai wasu ɗaiɗaikun ƙasashe da suke sa idonsu a kanta.

Idan muka waiwaya baya a tarihi, Nijeriya tana da jajirtattun mutane da suka yi gwagwarmaya a fannoni daban-daban na addini da siyasa don ganin ƙasar ta kafu, ta kuma tsaya da ƙafafunta. Hatta da Turawan mulkin-mallaka sun shaida cewa Nijeriya babbar ƙasa a Afrika da al’ummar cikinta suka bambanta da sauran al’ummar Afrika, ta fuskar al’adu masu kyau da kuma sana’a, baya ga ƙaunar juna da riƙo da addini.

Lokacin da Turawan Burtabiya suka shigo yankin Arewa da ƙudurorinsu, tabbas sun sha mamakin yadda suka samu al’ummar Hausa-fulani suna da abubuwa da dama na gudanar da rayuwa a cikin tsari, kamar su; sana’o’i da suka haɗar da noma, kiwo, kasuwanci da kasuwanni, zumunta, al’adu, tufafi da sauransu. Don haka wannan dalili ya sa suka girmama Hausawa, kuma suka ba su daraja, saɓanin abokan zamanmu na kudu waɗanda suka je suka same su babu sutura a jikinsu sai ganye da fatun namun daji da suke yin amfani da shi wajen rufe jikinsu.

Na yi duk wannan bayani ne saboda a fahimci yadda mu da kanmu muka yi wa kanmu illa a Nijeriya (musamman yankin Arewa).

Bayan duk shugabannin mulkin soja sun ƙare a Nijeriya, an ci gaba da mulkin Dimokraɗiyya a cikin ƙasa, mulkin da ake ganin an fi samun ‘yanci da walwala a cikin ƙasa a kan mulkin soja. To amma kuma yadda su ‘yan siyasar suka gurɓata al’amura, hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar al’umma da dama. Domin ɗan siyasa zai yi amfani da kuɗi wajen neman a zaɓe shi, wanda hakan laifi ne a kundin tsarin mulkin ƙasa, haka nan ɗan siyasa zai ɗauki alƙawura da yawa na yi wa mutane aiki idan an zave shi, nan ma idan ya samu abinda yake nema sai ya manta da jama’a.

Idan mai mulki yana kan kujerar mulki babu mai iya taɓa shi, ko faxa masa gaskiya, ko nuna masa kuskuren da ya aikata, domin yin hakan zai sa a kama mutum a kulle, ko a kashe shi ma bakiɗaya. Sannan dokokin ƙasa ba sa yin aiki a kan shugabanni da masu riƙe da madafun iko a gwamnati don suna da wata doka ta kariya da suka yi wa kansu sai dai dokar tafi aiki a kan talaka ne kawai, hatta mai kuɗi idan yana da kuɗi zai yi amfani da kuɗin ya sayi ƙarya ta koma gaskiya don kawai ya zamana babu wanda zai hukunta shi ko da ya yi laifi.

Hakazalika jami’an tsaro za su aikata laifi su karya doka babu wanda zai ce musu uffan (in dai akan talaka suka yi yadda suke so), idan ka ga an yi hukunci a kan jami’in tsaro to ka tabbatar wani babba ya taɓa, ko ɗan babba, ko kuma ya tava wani ɗan siyasa.

Sai ya zama a Nijeriya duk abinda mutum ya aikata na laifi zai iya fansar kansa matuƙar zai ba da kuɗi. Wannan ɗabi’a ta son zuciya da rashin son gaskiya, su ne suka haifar mana da cin hanci da rashawa a Nijeriya, duk wanda ya yi shuhura ya zama wani a ƙasar nan, to baya tavuwa idan dai har zai buɗe bakin aljihu.

Idan mai motar haya ya gogi motar Alhaji aka je wurin ‘yansanda sai a kulle mai motar haya saboda shi talaka ne matsiyaci, idan aka kama ɓarawon kaza ko biredi, ko buhun masara, ko wani abu makamancin wannan sai Alƙali ya tura shi gidan yari (bayan dukan da ya sha a hannun jami’an tsaro), idan wani ya yi wa wata ciki, ko fyaɗe, ko kisan kai, sai lauyoyi manya su bijiro suna kare shi (musamman idan yana da galihu), idan mutum attajiri ne ba ya tsoron ƙarya kowacce irin doka saboda yana da kuɗi.

Faruwar ire-iren waɗannan abubuwa a cikin ƙasa ya sa hatta shi kansa talaka sai ya fahimci shi ma idan ya karya doka kuɗi ne zai kuɓutar da shi, sannan kullum yana kallon shugabanni suna zalunci, jami’an tsaro suna yi, don haka shi ma don ya yi wa xan uwansa talaka zalunci bai yi laifi ba, ko don ya karya doka ba shi kaɗai yake karya ta ba. Wannan ne ya sa za ka ga idan ka zo kan sha-tale-talen ba da hannu mai danja mutane ba sa bin doka, idan ma’aikaci ne yake ba da hannu sai ya riƙe bindiga ko wata ƙatuwar sanda sannan mutane za su riqa tsayawa idan an tsaida su. Wasu suna ganin wannan wayewa ce amma kuma hakan hauka ne da rashin sanin ciwon kai da rashin kishin ƙasa.

Haka nan idan aka zo batun wasu abubuwa da ake yi na gwamnati don samar da haraji, wanda shi wannan harajin da ake biya ana tara kuɗin ne don yi wa al’ummar ƙasa aiki, kar mu kalli cewa wane bai yi ba, ko wane ba ya yi saboda shi jami’in tsaro ne ko na gwamnati, domin su ma da yawa sukan karya dokokin abubuwa da dama, shi ma talaka sai ya biye musu, duk da shi idan an kama shi yana shan wahala.

Don haka sai ka ga mutum yana ƙin biyan kuɗin wuta, ruwa, ƙin biyan kuɗin makaranta har a kori yaransa daga makaranta duk da cewa ilimin nan yana da amfani, da qin yin rijistar wasu abubuwa da ake yin rijista, masana’anta, ko kayan da ake sarrafawa, ko ƙin yin lambar abin hawa da takardu, ko ƙin bin dokokin hanya, da wasu abubuwa da ya kamata a ce komai ana yi bisa doka.

Don haka sai abubuwa suke ƙara lalace mana a Nijeriya, kowa inda ya sa gabansa daban, masu mulki sun sauka kan layi, attajirai da jami’an tsaro da na gwamnati, sarakuna sun saka son zuciya sun sauka kan layi, ‘yan kasuwa ma sun sa son zuciya sun sauka kan layi, talakawa sun sauka kan layi. Komai da ake yi ya zama kara-zube babu tsari, ba bin doka, babu tausayawa da sauƙaƙawa juna balle a kai ga maganar kishin ƙasa. Sai ya zama muna rayuwa ne ta kowa ya iya allonsa ya wanke, ba maza ba mata, mun zama kuɗi kawai muke buƙata, su ne abin tunaninmu dare da rana, kowa ya koma tamkar mai bautar kuɗi.

Muna gaggawar sai mun tara dukiya, mai kuɗi yana hangen na gabansa yana so sai ya kamo shi ko ya zarta shi, talakawa suna kallon mai kuɗi yana ajiyar zuciya da cije baki don hassada, mata sun saka buri da kwaɗayin duniya sai maikuɗi za su aura, mai mulkin siyasa ko sarauta, ko mai ɗamara ko wani hamshaƙin ɗan kasuwa mai Naira.

An shigo da al’adu waɗanda aka aro daga wasu ƙasashe da mutane daban-daban da ba mu haɗa komai da su ba. Duk wani abu da muke yi mun cuɗanya shi da baƙin al’amura da ba namu ba, kuma ba su zame mana tilas ba, amma mu mun maida su tilas a kanmu. Kowa yana so sai ya yi rayuwar jin daɗi da wadata, mun manta cewa kowanne bawa da abinda Ubangiji ya halicce shi da shi, da kuma arzikinsa a rubuce.

Mu kalli rayuwar da muke ciki a yau, mu tsaya mu yi nazari da tunani tsakaninmu da Allah, shin duk menene ya jefa mu a wannan halin? Na farko za mu ga akwai son zuciya da rashin tsayawa a kan doron doka da kuma matsayin da Allah ya ajiye mu, da rashin tausayi na shugabanni, da ma rashin tausayi na tsakaninmu da juna mu talakawa.

Mu kalli yadda komai ke canzawa, ɗan siyasa sai ya fitar da kuɗi ake zaɓarsa ko da bai cancanta ba, matuƙar zai ba da kuɗi za a zave shi ko da al’umma ba sa so. Ɗan kasuwa zai saye kayan noma wajen talakawa manoma ya ɓoye, sai lokacin buƙata ya yi yadda yake so, shi ma talakan ɗan kasuwa burinsa ya takura ɗan uwansa. Masu mulki da hukumomi, da ƙungiyoyi na kare haƙƙin ɗan Adam duk sun zama marasa amfani, kowa kuɗi da matsayi yake wa aiki.

Ta yaya muna cikin wannan rayuwar da muka ɗora kanmu za mu yi tunanin yin rayuwa cikin sauƙi? Ta yaya masu mulkinmu sun haɗa kai da Yahudawa da suke son mallakar qasarmu, yankinmu da muhallanmu za su bar mu muyi rayuwa cikin jin daɗi? Kai da ka zavi ɗan siyasa ya hau kujerar mulki bayan ka karɓi kuɗinsa kafin ka zaɓe shi, ko karɓa baka zaɓe shi ba kuma ya sani, yasan don abin hannunsa ka zave shi, ta yaya zaka zauna kana zuba ido da sa ran zai yi maka abinda zaka ji daɗi? Su kansu delagate ɗin ƙasarmu (musamman na Arewa) sai sun karɓi maƙudan kuɗaɗe a wajen ɗan takara suke mara masa baya, babu ruwansu da ya cancanta ko bai cancanta ba, me zai yi wa yankinsu idan ya hau kujerar mulki? Babu ruwansu da wannan, kashe ku za a yi, binne ku da ranku za a yi, yunwa da fatara gami da talauci za a saka muku? Duk babu ruwansu da wannan, kawai ya za a yi ya ba su kuɗi su mara masa baya, kamar dai irin abinda yake faruwa a Nijeriya yanzu.

Don haka, waɗannan tarin matsalolin da muke da su, wallahi tallahi su kaɗai sun isa su saka mu cikin masifa da bala’i a Nijeriya, tunda mu kalli yadda kullum farashin kayayyaki yake tashi, farashin yau daban na gobe da jibi daban, sai an yi magana mu riqa cewa Dalar Amurka ta tashi, bayan wani abin ma sam ba shi da alaƙa da wata dala, son zuciya ne kawai da neman tara abin duniya, ba ga mu talakawa ba haka ba ga su attajirai ko ‘yan kasuwa ba. Ita gwamnati dama ba ta tamu suke yi ba, itama tana da tata ajandar da kwangilar da take yi da ƙasashen da suke buƙatar wani abu a ƙasarmu, don haka babu ruwansu da halin da talaka yake ciki.

Sannan dole a ƙirƙiri wasu miyagun abubuwa da za su sa tunaninku ya taƙaita wuri ɗaya, shi ne abinda za ku ci. Sai a ɗauko wani gagarumin abu a danƙara muku, ya hana ku tunanin shin ina arzikin ƙasarku? Kuɗin da ake tarawa na albarkatun man fetur da wutar lantarki da sauran abubuwa na ma’adanai dake haƙowa a ƙasarku ina ake kai kuɗin?

Wannan tunanin dole sai an raba ka da shi, sai a kawo maka Boko Haram, satar mutane da garkuwa da su don neman kuɗin fansa, ƙarin kuɗin man fetur, gas da kalanzir, a cire tallafin mai a zo daga baya a ce za a ƙara kuɗin wutar lantarki, a ƙara wa kamfanoni haraji su kuma su ƙara kuɗin kaya, a karya darajar Naira a fifita Dala, duk wani abu da za ka siyo daga ƙasashen turai a ce sai da Dala.

Ga shi dai muna gani a ƙasarmu, an saka wasu jinsin mutane da suke cikinmu suna kashe manoma, suna tare hanya suna ɗauke mutane suna shiga daji da su, a Arewacin Nijeriya ake yin wannan. A yankin gabaci kuma an kafirta karatun boko, an kashe dubban mutane a sanadin haka, sannan an wayi gari yau ana fama da wata rayuwa mai tsada, wadda duk ga dalilaina nan a sama na faɗe su, kuma haka abin yake. Gashi nan yanzu kowa ta abinci yake, abincin kuma yana ƙara tsananin tsada, kuma a nan ƙasarmu duk ake noma shi.

To tambayar a nan ita ce, me ya sa ba za a buɗe iyakokin ƙasa ba? Me ya sa lokacin baya da iyakokin ƙasar suke a buɗe shinkafar ƙasar Thailand ba ta wuce 7,500 bayan an biya kuɗin dakonta ta yi wata da watanni kafin ta zo Nijeriya? Me ya sa tamu da ake nomawa a cikin ƙasa yau ta haura 50,000? Me ya sa ake kashe manoma a ƙauyuka ana ƙone musu gari, ana kore dabbobinsu? Me ya sa ake ƙara wa kaya farashi?

Me ya sa manyan jami’an tsaro kowa ya kama bakinsa ya yi shiru a kan abinda yake faruwa a ƙasarmu? Ina hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa? Ina hukumar kare haƙƙin ɗan Adam? Ina hukumomin ƙungiyar leburori da ma’aikatan ƙwadago? Ina ‘yan majalisarmu na dattijai da na wakilan al’umma? Ina Alƙalai da lauyoyi da sauran ƙungiyoyi masu cewar suna yaƙi don al’umma ta samu ‘yanci?

Saboda haka, babban ƙalubalenmu a Nijeriya shi ne rashin sanin ciwon kai, rashin bin doka da oda, son abin duniya ta kowacce hanya, da rashin tsayawa mu yi karatu a kowanne fanni, da kuma uwa uba rashin ɗaukar sana’a da muhimmanci, baya ga son banza da kwaɗayin abin hannun masu mulki da masu kuɗi. Ina faɗa muku wallahi tallahi sai mun gyara kanmu idan muna so ƙasarmu ta gyaru, sai mun shiga taitayinmu, sai mun sa ƙaunar juna da cire kwaɗayi ƙasarmu za ta gyaru.

Dole idan muna son mu samu kwanciyar hankali a ƙasarmu mu kawo sauyi, sauyin kanmu da sauyin jagorori a dukkan matakai. Sai mun sa ido sosai a kan ƙasashen da suke neman saye ƙasarmu da yankinmu don buƙatun kansu. Wannan yunwar da ake yi da gangan aka ƙaƙaba mana ita, aka sanya mana ita don mu fita hayyacinmu, su kuma waɗanda suka yi hakan su ci gaba da kwashe arzikin ƙasarmu suna kaiwa tasu ƙasar, ba su da wani fata a gare mu da ya wuce su lalata ƙasarmu, su ɗaiɗaita yankinmu na Arewa, su rusa mana addini da al’adu, mu dawo maƙasƙanta kuma mabarata.

A zahirin gaskiya mu yi karatun ta-nutsu mu san me muke yi, musamman mu ‘yan Arewa, domin tabbas akwai ajandar rusa mu da yankinmu, shi ya sa ake ganin wasu manyan abubuwa masu muhimmanci suna tashi daga Arewacin ƙasar nan ana maida su yankin kudu. To wallahi mu dawo hayyacinmu, mu san inda yake mana ciwo. Tilas mu tashi tsaye mu kawo ƙarshen duk wani tuggu da makirci da ake shiryawa, mu talakawa ne ya kamata mu yi wannan yaƙin na ceto yankunanmu da al’ummarmu, idan ba haka ba to lallai nan gaba abincin ma da za mu ci sai ya gagare mu ko da kuɗinmu.

Nafi’u Salisu
(Marubuci/Manazarci) daga Kano
nafi’[email protected]
[email protected]
Lambar tarho – 08038981211

By Editor