Tare da AMINA YUSUF ALI
Barkanmu da sake saduwa a wani makon a shafinku mai albarka na zamantakewa. Da ke zuwar muku kowanne mako a jaridarku ta Blueprint Manhaja. A wannan karon muna tafe da wani batu mai nauyi da muka yi bincike a kansa muka gano yana da matuƙar tasiri wajen gyarawa da rusa aure.
Kodayake, a ƙasar Hausa wannan magana ce mai ɗan nauyi, amma a binciken da muka yi a ‘yan shekarun nan matsala jima’i na daga cikin matsalolin da suke lalata rayuwar aure. Ire-iren matsalolin sun haɗa da rashin ita kanta mu’amalar aure, rashin lafiyar gaɓoɓin yin mu’amalar, sihiri, tasirin kallon finafinai baɗala, da sauransu. Amma a yau, ina so na mai da hankali ne a kan matsalar da kallon finafinan baɗala ya haifar a wannan zamanin.
A Yau yana wahala a ce akwai saurayi matashi ko yarinya matashiya da ba su taɓa ƙyalla ido a kan wannan fim na baɗala d suke yawo kamar banza ba a intanet. Kusan duk a cikin mutum 10, to 8 sun tava kallo, ko da sau ɗaya ne, ko sau biyu, ko ma fiye da haka. Wasu ba sun kalla ba ne da niyyar ci gaba da kallo, ko don suna so. Sun kalla ne wataƙila saboda sun ji wani ya yi zancen, ko kuma sun ci karo da shi wajen kallon fina-finan Amurkawa, ko kuma don kashe kwar-kwatar ido (Allah ya tsare mu).
Kusan ya zama al’ada yanzu, idan matasa za su yi aure sai sun kalla, ko dai saboda su ga abinda suke jin labari, ko kuma saboda neman ilimi, wanda kuskure ne hakan. Domin kuwa Malamai magabata sun tabbatar mana da cewa lamarin tarayyar auratayya lamari ne daga Allah, kuma ɗan Adam ba ya buƙata a koya masa, Allah ne yake ba da ilimin idan lokacin ya yi. Shi ya sa idan ka balaga abu na farko da kake fara gani shi ne mafarki kana saduwa.
Fim ɗin baɗala ba shi ne ya dace ya koyarwa kai ilimin saduwa ba, saboda haka ne ma nake so a cikin wannan rubutu na bayyana mana wasu abubuwa da yawa da muke ji, ko muke gani, ko ake faɗa game da auratayya da kuma illar da fim ɗin baɗala yake bari a ƙwaƙwalwar mutane.
Kallon wannan fim na baɗala ya canza tunanin matasa da yawa, kai har ma da wasu manyan. Domin kuwa yanzu ana iya samun mace ta koka a kan cewa mijin ta ba ya iya gamsar da ita yadda take so. Ko kuma namiji ya ji a ransa idan bai laga-laga da mace ba, to bai cika namiji ba.
Ko kuma wasu su ji, ai kai ba jarumi ba ne sai idan za ka iya awa kaza, ko ka yi tarayya a dare sau kaza, shi ne ka cika jarumi. Hakan nan idan ka je kasuwannin magani, da kyamis-kyamis, za ka yi ta cin karo da maza suna karɓar magunguna Ƙarin ƙarfin maza don zaburar da kawunansu. Su ma matan ba a bar su a baya ba, domin kuwa ba sa zama ba tare da sun sha ko sun ci wani abu makamancin wannan ba.
Ba na manta labarin wata baiwar Allah da muka kashe aurenta saboda mijin ta yana shan magani ƙarfin maza sosai, a rana maganar bakwai ake zuwa goma. Wallahi wannan ne sanadiyya mutuwar auren.
Abin da mutane da yawa ba su sani ba shi ne: Jaridar Cosmopolitan ta wallafa wata hira da ta yi da jaruman finafinan baɗala su 40. A inda bayanansu suka nuna cewa shi fim din baɗala fim ne kamar kowane irin fim. Yana ɗauke da takardar labari, wato labari, aiwatarwa, ƙirƙirarren labari da sauransu.
70-85% na abubuwan da ake bayyanawa a finafinan ba gaskiya ba ce zalla, akwai zuƙi-ta-malle wato ƙirƙira. Za a iya nuna jarumi da jaruma sun shafe awa ɗaya zuwa biyu suna abu ɗaya, amma a bayan fage, sun tsaya sun huta sama da sau biyar. To amma a kyamara an yanke don kar ka gani. Saboda haka ake so ka yarda.
Suka qara da cewa, ba don suna haɗawa da magani ba, da ko minti 10 ba za su iya yi ba, kuma ba don taimakon kyamara ba, da shi ma hakan ba zai samu ba. Wata daga cikin wanda aka yi wa intabiyu ɗin ta qara da cewa, ko iface-iface da suke yi, saka su ake yi don ƙara wa masu kallon armashi.
Ta ƙara da cewa, wasunsu, a cikin tsananin zafi suke, saboda abin ya wuce hankalin da kuma maqurar da jikin ɗan adam zai iya ɗauka. Don haka Darakta ne zai ta cewa a yi ta ihu don a inganta sin ɗin da ake yi. Don haka, ba gaskiya ba ne. Wani jarumi shi ma ya tofa albarkacin bakinsa inda ya ce, shi mai aure ne, kuma tunda yake saduwa da matarsa, bai tava wuce minti 20 ba. Wanda idan da kuwa a fim ne, har mai awa uku ya yi.
Idan ka koma vangaren litittafen Hausa, su ma sun taimaka ƙwarai wajen sanya wa matasa tunani makamancin wancan, da burika wajen mu’amalar auratayya. Wannan shi ma koma-baya ne sosai, domin kuwa mata sukan kalli mazajensu a matsayin malalata, ragwaye, marasa kuzari, saboda su a tunaninsu, namiji shi ne wanda yake kai wa minti 30 zuwa awa ɗaya.
Sannan bayan ya sauka, ya sake komawa, idan ya sauka ya sake, aƙalla sau uku ko huɗu kafin Asuba. Tabbas akwai maza jarumai waɗanda za su iya haka. To amma tambaya a nan shi ne, meye matsayin hakan a lafiyance sannan da kuma addini?
Ya zo a cikin Sahih Bukhari, Manzon Allah SAW yana cewa mu guji yin abubuwa su wuce iyaka, domin duk abinda ya wuce hankali yana zama cuta ne ga ɗan adam. Jaridar Ingilishi ta PlayBoy ta Amurka ta wallafa wani bincike da ta yi a kan adadin mutanen da ya kai dubu huɗu, a inda binciken nunawa cewa kaso 50% daga cikin waɗanda aka yi binciken kansu kaxai ne suke iya kai wa mintuna 9 da daƙiƙu 40 a lokacin saduwa.
Kaso 30% kuma minti 14 da daƙiƙu 10. Kaso 20% kuma mintuna 20 dai-dai. Sai masana suka ƙarƙare cewa, matsakaici adadin mutanen duniya a yadda Allah ya tsara halitta, ba sa wuce minti 4 zuwa minti 9 a lokacin saduwa (Saduwa a nan yana nufin sanda aka haxe turmi da tabarya). Sannan mafi yawancin mutanen duniya suna saduwa ne sau uku kacal a kowane sati. Kaɗan ne daga cikin mutane suke iya yi kullum ko kuma fiye da sau ɗaya a kowane wuni. Amma dai bayanai suna nuna cewa akwai matsala sosai a ce ɗan adam ya yi jima’i fiye da sau uku a wuni ɗaya.
Bayanai sun nuna cewa masu yin jima’i sama da 5 zuwa bakwai suna fuskantar wata cuta mai sanya ƙwayayen ɗa namiji su fara fitar da jini a maimaikon maniyyi. Sannan yi ɗin da yawa ta hanyar amfani da maganin sanya dadewa yana kawo mutuwar gaba ta din-din-din bayan shekaru sun ja.
Don haka, ina so na ja hankalin ma’aurata da su sani cewa, abinda suke karantawa a littafi ko suke kallo a fim, ba wani abu ba ne illa shirin fim ne kawai. Shiri ne don ƙayatarwa da nishaɗatarwa. Sannan binciken masana ya nuna kamar yadda ya zo a mujallar Ingilishi ta PentHouse cewa ma’auratan da suke ta’ammali da finafinai na baɗala ba sa iya gamsar da juna a lokacin saduwa.
Jaridar ta ƙara da cewa, wannan matsalar tana haddasa mutuwar aure da kaso 9% a ƙasar Amurka duk shekara. Sannan ta ƙara da cewa: bayanan sirri na masana’antar samar da bidiyo na baɗala sun nuna cewa masana’antar tana fuskantar ƙalubale na Shari’a da mutane da dama wanda suka ɗauka cewa abinda yake faruwa a finafinan gaskiya ne, domin a cewar su, ya shammace su kuma ya lalata musu rayuwar aure.
Bari na dakata a nan. Allah ya bamu ikon faɗin gaskiya da kuma aiki da ita, ya kuma ganar da mu gaskiya duk rintsi, sannan ya kare mana idanuwanmu daga zinar ido.
Muhammad Ubale Ƙiru, baƙon marubuci ne a shafin zamantakewa na wannan mako. Allah ya saka masa da alkhairi ya ƙaro basira, ya sa al’ummarmu su amfana da wannan rubutu. Sai wani makon idan Allah ya kai mu.
