Ramadan: Al’ummar Kebbi za su yi azumi cikin wadatar wutar lantarki

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Kebbi, Gwamna Nasir Idris, ya yi zama da kamfanin lantarki KAEDCO inda suka tattauna yadda za a samar da wutar lantarki na sa’o’i 24 kulli yaumi a faɗin jihar yayin watan Ramadan mai zuwa.

Da yake jawabi yayin tattaunawar, Gwamna Idris ya nuna matuƙar damuwa kan yadda ake fana da ƙarancin wutar lantarki a jihar.

Ya ce sun cimma yarjejeniya da KADECO kan yadda za a tabbatar da wadatar wutar yayin azumin Ramadan domin bai wa al’ummar jihar damar yin azumi da cikin walwala.

“Na gayyaci Manajin Darakta na KAEDCO don tattaunawa. Akwai buƙatar mu faranta wa al’ummar Jihar Kebbi State,” in ji Gwamman.

A baya Gwamnatin Jihar Kebbi ta sha alwashin raba wa talakawan jihar abinci kyauta a ƙarƙashin shirinta na ciyarwa lokacin Ramadan.

Kwamishin Harkokin Noma na jihar, Alhaji Shehu Mu’azu, ya bayyana wa manema labarai cewa gwamnati ta kammala shiri raba man fetur kyauta ga manoman da za su yi noman rani don sauƙaƙe tsadar farashin amfanin gona a jihar.