Ghana na bikin cika shekara 67 da samu ‘yancin kai

Daga BASHIR ISAH

A wannan Larabar ƙasar Ghana ke bikin cika shekara 67 da samun ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka.

Ghana ta shafe shekara 83 a ƙarƙashin Turawan mulkin mallaka kafin daga bisani ta samu ‘yancin kanta.

Shugaban ƙasar na farko, Dr Kwame Nkrumah, ya bayyana samun ‘yancin ƙasar a matsayin babban cigaba gane da shugabancin ƙasar.

Ranar 6 ga Maris ta kowace shekara Ghana ke bikin ranar zagayowar samun ‘yancin kai.

Bikin wannan karon zai gudana ne a dandalin Youth Resource Centre da ke Koforidua.

A 2017 ne Shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya ɗauki matakin jujjuya in wurin da bikin ranar samun ‘yancin kan zai riƙa gudana donin baje kolin irin arzikin da kowane shiyya ke da shi.