Batun aiwatar da rahoton ‘Oransaye’

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince a aiwatar da rahoton kwamitin Stephen Oransaye.

Wannan na daga cikin abubuwan da aka cimmawa a taron Majalisar Zartarwar Tarayya na ranar Litinin 26 ga watan Fabrairu, wanda shugaba Tinubu ya jagoranta a Abuja.

Rahoton Stephen Oransaye na shekarar 2012 ya bayar da shawarar haɗe wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati waɗanda ayyukan su ke da alaqa da juna, a wani mataki na rage kuɗin da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati.

Bayan taron Majalisar Zartarwar ne hukumomi suka fitar da sanarwa inda suka ce an yanke hukuncin aiwatar da rahoton Steve Oronsaye domin sauya fasalin wasu hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya.

Sanarwar da mai taimakawa shugaba Tinubu na musamman a kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X ta ce, gwamnati za ta tsaya haiƙan domin ganin ta aiwatar da rahoton saboda amfanin shi, duk da cewa zai ƙunshi rushe wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayyar da kuma narke masu aiki iri ɗaya da juna a wajen guda.

Sanarwar ta ce “Shugaban ƙasa ya amince da kafa wani kwamitin mutum 8 wanda zai tabbata an bi duk ƙa’idar da ta kamata wajen yin gyare-gyaren da suka dace wajen aiwatar da rahoton.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, da yake jawabi ga manema labarai a fadar shugaban ƙasa a ranar Litini, ya ce “a cikin wani gagarumin yunƙuri a yau, gwamnatin shugaban Tinubu ta ɗauki matakin aiwatar da rahoton da ake kira Oronsaye Report don amfanin Nijeriya”

“Yanzu, abin da hakan ke nufi shi ne, an soke wasu hukumomi da kwamitoci, da wasu sassa a zahiri. Wasu kuma an gyara su, kuma an yi musu alama yayin da wasu kuma an rage su. Wasu kuma, ba shakka, an ɗauke su daga wasu ma’aikatun zuwa wasu inda gwamnati ke ganin za su yi aiki sosai.”

Kwamitin ya ƙunshi sakataren Gwamnatin Tarayya da shugabar ma’aitan gwamnati da ministan shari’a da ministan kuɗi da shugaban hukumar gyaran aikin gwamnati da mai taimakawa shugaban ƙasa a kan majalisar dokokin tarayya da ofishin kula da majalisar zartarwa,” inji Onanuga.

A 2011 ne shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya kafa kwamitin da zai yi nazari kan hanyoyin yin gyaran fuska ga tsarin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya a ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ma’aikatan tarayya, Stephen Oronsaye.

Kwamitin ya ƙunshi mutane kamar haka- Stephen Oronsaye a matsayin shugaba, da Japh CT Nwosu da Rabiu D. Abubakar da N. Salman Mann da Hamza A. Tahir da Adetunji Adesunkanmi da kuma Umar A. Mohammed duk a matsayin mambobi.

A watan Afirilun 2012 kwamitin ya gabatar da rahoton sa mai shafi 800, inda ya ce Gwamnatin Tarayya tana da ma’aikatu da hukumomi da kuma cibiyo 541.

Rahoton ya bankaɗo irin hamayyar da ke tsakanin hukumomi da ma’aikatun gwamnati da dama masu aiki iri ɗaya, abin da kuma ya ce yana kawo cikas ga ingancin aiki da kuma varnar dukiyar ƙasa.

Kwamitin ya bayar da shawarar a yi tankaɗe a hukumomin gwamnati 263, ta yadda za su koma 161, da rushe wasu hukumomin 38 da kuma haɗe wasu cibiyoyi da rassan gwamnati 14.

Haka nan kuma, rahoton ya bayar da shawarar gwamnati ta daina ɗaukar ɗawainiyar cibiyoyin ƙwararru, matakin da ya ce zai bayar da damar kashe kuɗin wajen gudanar da manyan ayyuka a sassan ƙasar.

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan bai aiwatar da wannan rahoto ba, amma a watan Maris ɗin 2014 ya kafa wani kwamiti ƙarƙashin ministan shari’a, Mohammed Adoke wanda ya ɗorawa alhakin tsara yadda za a aiwatar da rahoton.

Bayan shiga ofis a 2023 ne shugaba Tinubu ya sanar da cibiyoyi da ƙungiyoyin ƙwararru cewa gwamnati za ta daina ɗaukar nauyin su daga lokacin da za ta fara aiwatar da kasafin 2024, kamar yadda kwamitin shugaban ƙasa a kan albashin ma’aikata ya bayar da shawara.

“Ina sanar da ku cewa kwamitin shugaban ƙasa a kan albashi a yayin taron sa na 13 ya amince da dakatar da ɗaukar nauyin ƙungiyoyi da cibiyoyin ƙwararru daga ranar 1 ga watan Janairun 2024. Hakan na nufin daga wannan rana za ku kula da ayyukan ku da kan ku,” inji shugaban ƙasar.

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ma ya sha alwashin aiwatar da rahoton na Oronsaye, bayan hawan sa mulki a 2015.

Gwamnatin shugaba Buhari ta kafa kwamitin Bukar Aji domin sake yin nazari a kan rahoton bayan aikin da kwamitin da tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya kafa ya yi a baya.

A lokacin da aka gabatar da rahoton Oronsaye, Gwamnatin Tarayya tana da hukumomi 541 ne, amma a yanzu sun ƙaru.

Hukumar tsara albashin ma’aikata za ta koma ƙarƙashin hukumar haraji. Majalisar dokokin tarayya za ta buƙaci gyara kundin mulki domin tabbatuwar wannan domin kundin ne ya kafa hukumar harajin.

Za a haɗe Hukumar Kula da Kayayyakin Gwamnati da Hukumar Da Ke Kula Da Kayan More Rayuwa ta Ƙasar. Za a koma kira ta Hukumar Kula da Kamfanoni da Kayayyakin Gwmanati.

Hukumar Kare ’Yancin Ɗan Adam za ta Haɗe da Hukumar Ƙorafin Al’umma.

Hukumar bayar da agajin gaggawa, NEMA za ta haxe da hukumar kula da ’yan gudun hijira kuma za a riƙa kiran ta hukumar agajin gaggawa da kula da ‘yan gudun hijira ta ƙasa.

Hukumar kula da al’ummomin kan iyakar ƙasa za ta zamo wani sashi a ƙarƙashin hukumar kula da kan iyaka.

Za a haxe Hukumar Yaƙi da Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki da Hukumar Hana Yaɗuwar Cutuka ta Ƙasa.

Hukumar tabbatar da ingancin aiki za ta zamo wani sashi a ƙarƙashin hukumar gyaran ayyukan gwamnati.

Hukumar kula da ƙasar noma za ta koma ƙarƙarshin ma’aikatar noma da wadata ƙasa da abinci.

Ma’aikatar Kimiyya ta Tarayya za ta kula da wata sabuwar hukuma da za ta ƙunshi NCAM da NASENI da kuma PRODA.

Hukumar kula da gidajen tarihi da hukumar kula abubuwan tarihi ta ƙasa za ta narke ta zama hukumar gidajen tarihi da kula da kayyakin tarihi ta ƙasa.

Cibiyar wasan kwaikwayo ta ƙasa za ta haɗe da hukumar raye-rayen al’adun ƙasa.

Gidan Rediyon Tarayya da Muryar Nijeriya za su haɗe su zamo Hukumar Yaɗa Labarai Ta Nijeriya.

Cibiyar Sarrafa Fatu ta Ƙasa da Cibiyar Sarrafa Sinidarai ta Ƙasa za su haɗa domin zama hukuma ɗaya.

Hukumar Bunƙasa Magunguna da Hukumar Bincike da Nazarin Magunguna Ta Ƙasa su haɗe su zamo hukuma ɗaya.

Cibiyar Nazarin Bunƙasa Ƙarafa ta Ƙasa za ta haɗe da cibiyar Horar da Dabarun Sarrafa Ƙarafa ta Ƙasa.

Cibiyar Nazari Kan Cutar Bacci za ta koma ƙarƙashin Cibiyar Binciken Lafiyar Dabbobi ta Vom a Jos.

Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tsaya tsayin daka wajen ganin an aiwatar da wannan rahoto yadda ya kamata.