EFCC ta kama manyan motoci 21 maƙare da kayan abincin fasaƙwauri a Borno

Daga BASHIR ISAH

Hukumar EFCC ta ce ta kama wasu manyan motoci guda 21 maƙare da kayan abinci da sauransu wanda aka yi nufin fitarwa zuwa N’djamena a Jamhuriyar Chadi da kuma Kamaru ba bisa ƙa’ida.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fita a ranar Talata, inda ya ce jami’an da ke aiki qarqashin ofishin hukumar na shiyyar Maiduguri ne suka kama motocin a yankunan Kalabiri/Gamboru Ngala da Bama a Jihar Borno.

Oyewale ya ce za a gurfanar da waɗannan aka kama da motocin a kotu da zarar an kammala bincike.

A cewar sanarwar: “Bincike ya nuna killace kayan abincin a cikin motocin ne ta yadda muddin ba lura aka yi ba za gane ba har dai a samu a fita da su, amma jami’an hukumar sun samu nasarar gano kayayyakin.

“Kuma takardar shaidar kayayyakin ta nuna za a tafi kayan ne zuwa N’djamena da ke Jamhuriyar Chadi, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Kamaru,” in ji sanarwar.