Boko Haram ta ƙona gomman gidajen ‘yan gudun hijira a Borno

Daga BASHIR ISAH

Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari tare da ƙona gidaje sama da 25 da aka gina wa ‘yan gudun hijirar da suka koma matsuguninsu a yankin Ƙaramar Hukumar Dikwa a Jihar Borno.

Daily Trust ta rawaito cewar, matsalar rashin tsaro ta sa mazauna Dikwa sun gudu sun bar gidajensu zuwa neman mafaka a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Ta ƙara da cewa, kwanaki kaɗan bayan da suka yi garkuwa da wasu ‘yan gudun hijira da suka tafi neman itacen hura wuta a daji, ‘yan bindigar sun kuma kai hari a ƙauyen Gajibo inda suka yi harbe-harben bindiga tare da ƙona sabbin gidajen da aka gina wa ‘yan gudun hijira guda sama da 25.

Majiyar tamu ta ƙara da cewa, wani ganau, Modu Kundiri wanda ke kan hayarsa ta zuwa Maiduguri daga Gomboru a lokacin da lamarin ya faru, ya ce, sojoji sun buƙace su da su tsaya a ƙauyen Logomani na tsawon sa’o’i uku.

“Sojoji sun sanar da cewa akwai buƙatar mu dakata na kimanin sa’o’i uku, daga ƙarfe 11 na safe 2 na rana kafin aka ba mu damar barin Logomani.

“Na gani da idanuna, kuma na ƙirga gidaje sama da 25 da aka a ƙauyen Gajibo a yankin ƙaramar hukumar Dkiwa,” in ji Modu.

Gajibo gari mai tazarar kilomita 110 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.