Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif, ya rantsar da sabbin alƙalai a matakan kotunan jihar daban-daban.
Alƙalan da rantsarwar ta shafa sun haɗa da alƙalan Babbar kotun Jiha guda tara da kuma alƙalan kotun ɗaukaka ƙara na shari’ar Musulunci guda uku huɗu, bayan da Hukumar Kula da Shari’a ta Ƙasa (NJC) da kuma Majalisar Dokokin Jihar Kano suka amince da naɗin nasu.
Sanarwar da Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta ce, waɗanda aka naɗa a matsayin alƙalan Babbar Kotun Jihar su ne, Justice Fatima Adamu, Justice Musa Ahmad, Justice Hauwa Lawan, Justice Farida Rabi’u Dan Baffa, da kuma Justice Musa Dahiru Muhammad.
Sauran su ne: Justice Halima Aliyu Nasir, Justice Aisha Mahmud, Justice Adam Abdullahi, da kuma Justice Hanif Sunusi Yusuf.
Alƙalan kotun ɗaukaka ƙara na shari’ar Musulunci da aka naɗa kuma, akwai Khadi Muhammad Adam Kademi da Khadi Salisu Muhammad Isah da Khadi Isah Idris Said da da kuma Khadi Aliyu Muhammad Kani.
Da yake jawabi ga alƙalan a wajen bikin rantsarwar da aka gudanar a ɗakin taro na Africa House dake Fadar Gwamnatin Kano a ranar Juma’a, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce an yi naɗin ne a bisa cancanta, inda naɗin nasu ya zama shaida da ke nuna ƙwarewar su ta fuskar shari’a da jajircewarsu wajen tabbatar da adalci da kuma bin doka da oda.
A cewar Gwamnan Kano, “Haƙƙin da kuka ɗauka yana da yawa, kuma tasirin hukuncinku ya kai ko’ina. Wannan nauyi ne da ke buƙatar ba wai kawai ƙwarewar shari’a ba har ma da zurfin fahimta, tausayawa da jajircewa wajen kiyaye muhimman ƙa’idoji waɗanda aka gina tsarin shari’ar mu a kansu”.
Alhaji Abba Kabir ya ci-gaba da cewa, tun da aka kafa gwamnatinsa ta amince da mafi yawan buƙatu daga ɓangaren shari’a da ke da alaƙa da ƙudirin gwamnatin sa na raba madafun iko da ‘yancin kan ɓangaren shari’a.
Sannan ya buƙaci alƙalan da su yi aikin su cikin tsoron Allah, tausayawa da jajircewa wajen yin hidima tare da bayyana kyakykyawan fata a gare su dangane da wannan sabon nauyi da ya hau wuyan su.
Bikin Rantsuwar dai ya sami halartan Babbar Alƙalin-alƙalan jihar Kano, Mai shari’a Dije Aboki, Grand Khadi na Kano, Khadi Tijjani Yusuf Yakasai, Alƙalai da sauran jiga-jigan dake fannin shari’a daga ɓangarori daban-daban na ciki da wajen jihar.
