‘Yan bindiga sun yi garkuwa da gomman ɗaliban tsangaya a Sakkwato

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga jihar Sakkwato sun ce, ‘yan bindiga sun sace gomman ɗalibai a wata makarantar tsangaya da ke yankin Gidan Bakuso a ƙaramar hukumar Gada da ke jihar.

Majiyarmu ta ce an yi awon gaba da ɗaliban ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare.

Mai makarantar, Malam Liman Abubakar, ya shaida wa majiyar tamu cewa, ba a ga wasu ɗailibai su 15 ba, kuma ana ci gaba da ƙirga ɗaliban da suka ɓata.

Abubakar ya ƙara da cewa, yayin harin ‘yan bindigar sun harbi mutum guda da bindiga sannan sun ɗauki wata mata.

Ya ce “A lokacin da maharan suke ƙoƙarin ficewa daga garin sai suka hangi ɗalibanmu na rugawa zuwa ɗakunansu, kuma sun yi garkuwa da wasu da dama.

Wata majiya ta shaida wa News Point Nigeria cewa, kiman ɗalibai dozin biyu ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.

Ɗan majalisa mai wakilta mazaɓar Gada ta Gabas a Majalisar Dokokin Jihar, Kabiru Dauda ya tabbatar da aukuwar harin.

Wannan na zuwa kwanaki kaɗan bayan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da ɗaliban firamare sama da 200 a jihar Kaduna.

By Editor