Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Ranar Talatar da ta gabata ne a Jihar Kebbi aka rantsar da ƙarin kwamishina ɗaya da shugabannin riƙo na ƙananan hukumomi 21 da ke akwai bayan rushe majalisun ƙananan hukumomin a cikin watan da ya gabata.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala rantsar da shugabannin, Gwamna Nasir Idris ya yi kira ga al’ummar jihar Kebbi da su ci gaba da bai wa wannan gwamantin goyon baya don ganin ta aiwatar da ayyukan ci gaba da ta yi alƙawari a baya lokacin yaƙin neman zaɓe.
“Wannan gwamnatin ta kowa da kowa ce da matasa da kuma dattijawa kuma a haka za ta ci gaba da rabon muƙamai in Sha Allahu ta yadda ba wani ɓangare da zai ga an mayar da shi saniyar ware.”
Ya ƙara da cewa “wannan gwamnati ce mai adalci da ke karɓar bayanai daga mutane daga kowane ɓangare da kuma mataki, bayan wannan kuma tun kafin ya zamo gwamna ya san akalla kashi saba’in na matsalar jihar saboda haka ba za mu zauna mu ce sai an gaya mana abinda za mu yi ba, ni cikakken ɗan jihar Kebbi ne kusan dukkanin rayuwata na yi ta ne a cikin wannan jiha ku da kanku masu shaida ne akan haka, muna zantawa da masu ruwa da tsaki na jiha daga kowane mataki na jiha da qananan hukumomi wanda a iya cewa na san kashi saba’in da biyar na matsalolin jihar Kebbi. Don haka bana buqatar sai an yi min bayanin inda matsala take,” in ji shi.
Ya yi kira ga sababbin shugabannin ƙananan hukumomin na riqo da su sani cewa lokacin da shugaban ƙaramar hukuma zai zauna babban birnin jihar wato Birnin Kebbi ya wuce dole ku koma ga ƙananan hukumomin ku kusan mutane su san ku ku taimaki mutanen ku wannan mataki ne na gwaji kodai ku koma ku yi abinda ya dace ko mu nuna ma ku hanyar fita.
“Daga ƙarshe ina taya ku murna tare da Kwamishinan da ya karɓi rantsuwa yanzun nan murna muna sane da kyawawan tarin ayyukanku kuma a yau kyawawan ayyukan ka ne suka zamemaka tsani muna tayaku murna dukanku.”
Bello Hassan (Gaga) ɗaya daga cikin shugabannin ƙananan hukumomin daga ƙaramar hukumar mulki ta Augie ya jaddada mubayi’an su ga gwamnatin Dr Nasir Idris Ƙauran Gwandu da kuma alƙawarin biyayya ga doka da oda da ɗa’a ga gwamnatin.
Ya ƙara da cewa in Sha Allahu ba za su bai wa gwamna kunya ba, za su tsaya su yi duk abinda ya dace wajen tabbatar da samun haɗin kan al’umma da kuma aiwatar da ayyukan ci gaba a yankunansu.
Ya kuma nemi haɗin kan al’umma inda ya ce a ko da yaushe ƙofofin karɓar shawarwari a buɗe suke saboda haka duk wani mutum da ke da wata shawarar da za ta kawo ci gaba to a shirye suke su karɓa.
