Ku nemi watan Ramadan daga ranar Lahadi — Sarkin Musulmi

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci a Nijeriya (NSCIA), Sa’ad Abubakar, ya buƙaci al’ummar Musulmi da a nemi jinjirin watan Ramadan na shekarar 1445AH daga ranar Lahadi, 10 ga Maris, 2024.

Umarnin hakan na ƙunshe ne a sanarwar da ke ɗauke da sa hannun Farfesa Sambo Janaidu wanda ya kasance Shugaban Kwamitin Shawara na Majalisar Masarautar Sakkwato wadda aka raba wa manema labarai a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce: “Ana sanar da Al’ummar Muslim kan cewa su fara neman jinjirin watan Ramadan daga ranar Lahadi, 10 ga Maris wanda ya yi daidai da 29 ga Sha’aban 1445 AH.”

Sanarwar ta buƙaci duk inda Allah Ya sa aka samu ganin jinjirin watan, a sanar da Dagaci mafi kusa don ɗaukaka sanarwar zuwa gaba.

By Editor