Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Dikko Umar Raɗɗa ta bayyana cewar za ta ciyar da al’umar jihar dafaffen abinci don yin buɗa-baki tun daga farko zuwa ƙarshensa azumin Ramadan na bana.
A cewar sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, za riƙa ciyar da al’umar jihar dubu 72,000 a kowace rana a cibiyoyi daban-daban da za a buɗe a faɗin jihar.
Hakan na nufin za a ciyar da mutane milyan 2,000,000 cikin watan mai alfarma na shekarar 1445 AH/2024.
Kazalika, Gwamnan Jihar ya ba da umurnin fara sayar da masara, gero da kuma dawa na gwamnati ga al’umar jihar kan farashi N20,000 kowane buhu, inji sanarwar.
Ya yi bayanin cewa gwamnatin jiha ta sayi buhu dubu saba’in da biyu da ɗari biyu (72,200) na masara da gero da dawa inda za a kai buhu ɗari biyu (200) a kowace mazaɓa daga mazaɓu 361 dake faɗin jihar nan.
A ƙarƙashin wannan shiri, Dikko Raɗɗa ya ce an yi tanadin rarraba ingantacen abinci domin buɗa-baki ga mutum 72,000 a sassan jihar.
Gwamna Raɗɗa ya kuma sanar da cewa, gwamnatinsa ta tanadi buhun shinkafa mai nauyin kilo 25, wanda za a raba kyauta ga mutane 33,000 da suka haɗa da masu bukata ta musamman da gajiyayyu da tsofaffi.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Katsina ta ɗauki waɗannan matakai ne don karya farashin abinci, wanda ya yi tashin gwauron zabi don kawo sauki ga al’umma.
Don haka, ya yi gargadin cewa dukkan shirye-shiryen an tanade su ne domin talakawa masu bukata, saboda haka ne ya yi gargaɗin kada a ga wani mai sukuni na ƙoƙarin saye, ko shiga layin amsar abin da za a rarraba wa masu rauni.
