CITAD ta gina ‘bukkar Intanet’ ta sama da Naira miliyan 30 a Jama’are

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Bauchi

Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al’umma CITAD ta samar da wata ‘bukkar Intanet”, kana ta damƙawa al’ummar garin Jama’are da ke Jihar Bauchi, aka kuma ƙaddamar da ginin bukkar a hedkwatar Ƙaramar Hukumar Jama’are ranar Asabar da ta gabata.

Babban Daraktan Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al’umma CITAD Engr. Yunusa Zakari Ya’u ya bayyana cewa a cikin wannan tsari mai taken Digital Hub za su gina ire-iren wannan bukka ta intanet guda 20 cikin shekara ɗaya a faɗin Nijeriya.

Y. Z. ya ce: “Kwamfutocin da ke cikin wannan bukka ba kamar sauran kwamfutoci ba ne, su suna ɗauke da Manhajar dukkanin darussan sakandire ta yadda idan wani abu ya shigewa ɗalibi ko malami duhu zai shiga wannan bukka ya koyi ilimi, duka dai don bunƙasa ilimin wannan yanki.”

Kazalika ya ce “Akwai ɓangaren koyon sana’o’i daban-daban wanda matasa maza da mata za su zo su buɗa su koyi sana’a, domin yanzu kamar na sha faɗa yanzu ba sai ka je cirani Legas ba kana zaune a gida za ka koyi sana’ar da za ta riee mutum da iyalinsa.

“Don haka nake fatan mutanen Jama’are za su yi ƙoƙari su yi amfani da wannan dama su koyi sana’ar dogaro da kai.”

Shi ma a nasa ɓangaren babban jami’i da ke kula da harkar sadarwa na al’ummomi (Commumity Network) Haruna Adamu Hadejia ya bayyana cewa aikin bukkar ya laƙume aƙalla miliyan 30 wajen gina shi.

Ya ce, “mun gina masu wannan bukka ne ko rumbu domin mun lura da cewa garin Jama’are na tsananin buƙatar sadarwa, a 2021 bincike ya nuna cewa akwai alƙaryu 114 da suke da matsala ta sadarwa kowane ƙauyuka idan ka duba za ka ga cewa a lissafin, ana ciki wannan hali.”

Haruna Adamu ya ƙara da cewa al’ummar garin Jama’are su ne suka jagoranci gina wurin da qarfinsu inda suka tallafa da yashi da siminti da ruwa da abincin ma’aikata da sauransu.

Muhammad Sabo Madakin Jama’are kuma shugaban kwamitin sadarwa na wannan bukka ya bayyana cewa waɗannan ƙungiyoyin huɗu da suka haɗu suka gina wannan bukkar, sun haɗu ne domin isar da hanyar sadarwa ta zamani wanda aka samu giɓinta a wasu wurare.

“Tabbas mu mutanen Jama’are mun yaba masu kuma mun gode da irin wannan ƙoƙari da suka yi mana,” in ji Madakin Jama’are.

Da take nata jawabin Malama Mairo Habu Ciroma wacce malamar makarantar sakandire ce ta ce, “lallai mun ji daɗi da aka kawo mana wannan bukka, kuma za ta amfanemu ta kuma amfani ɗalibanmu.

“Yanzu mu a makarantarmu muna fuskantar matsalar rashin cibiyar yin JAMB, yaranmu suna zuwa gari mai nesa wajen zuwa zana jarabawar, amma zuwan wannan bukka za mu haɗa gwiwa da CITAD domin a samar mana cibiyar JAMB,” inji Malama Mairo.

Wannan bukka ta intanet an sanya mata kwamfiyuta guda 8, sannan akwai hasken wutar lantarki ta solar, kuma wannan shi ne karo na biyu da waɗannan haɗaka ta wannan ƙungiyoyi huɗu suka gina.

Cibiyar CITAD da haɗin gwiwa ne da Hello World da 48% da kuma Association for Prograssive Communication (APC) ne suka ɗauki nauyin gina wannan bukka mai cike da tarihi da amfani ga al’umma.

By Editor