Daga DAUDA USMAN a Legas
A ranar Asabar ta makon jiya majalisar mai Martaba Sarkin Dakwa a Abuja, Alhaji Dakta Alhassan Musa Baba Chikuri ta yi naɗe-naɗen hakimanta a garin Abuja.
Alhaji Abdulrahaman Ishak Bin Aliyu Dotsa yana ɗaya daga cikin waɗanda majalisar ta naɗa, inda da amincewar Sarkin na garin Dakwa Dakta Alhaji Alhassan Musa Baba majalisar ta naɗa Alhaji Abdulrahaman Ishak Bin Aliyu a matsayin sabon Sarkin Fulanin garin Dakwa na farko.
Taron naɗe-naɗen sarautun wanda ya gudana a harabar fadar mai martaba Sarkin Dakwa Alhaji Alhassan Musa a ranar Asabar ɗin ƙarshen makon jiya.
Taron ya samu halartar ɗumbin al’ummar waɗanda suka fito daga sassa daban-daban na cikin garin Abuja da wajenta baki ɗaya waɗanda suka haɗa da sarakunan ƙabilu daban-daban dake cikin Abuja da sauran manyan baƙi da jami’an tsaro waɗanda suka haɗa da ‘yan sanda sojoji da sauransu.
Bayan kammala taron naɗe-naɗen, Manhaja ta zanta da sabon Sarkin Fulanin na farko a garin Dakwa ta wayar tarho Alhaji Abdulrahaman Ishak Bin Aliyu domin jin ta bakinsa dangane da wannan al’amari inda ya bayyana cewa haƙiƙa ya yi farin ciki da wannan sarauta, kuma zai bada duk gudunmuwar da ake buƙata don ganin an kawo ci gaba a yankin da fadar masarautar Dakwa.
