Man United ta fi nuna ƙwarewarta a Firimiya – Ten Hag

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Erik ten Hag ya bayyama cewa Manchester United ɗaya ce daga cikin ƙungiyoyin da ta fi nuna bajinta a gasar Firimiya ta bana.

Kocin ya faɗi hakan duk da ƙungiyar Old Trafford na fama da kalubalen cin wasa ko dai a gida ko a waje a kakar nan.

Ranar Asabar United ta tashi 1-1 da Burnley a firimiya, wadda take ta biyun ƙarshe, inda mai tsaron raga, Andre Onana ya yi kuskuren da aka farke a bugun fenariti ta hannun Zeki Amdouni.

Hakan na nufin Ten Hag ya samu nasarar wasa daya a cikin minti 90 tun daga cikin watan Maris da haɗa maki bakwai daga wasa shida baya.

An kuma ci ƙwallo 38 a wasa shida bayan nan da United ta buga da wasu ƙungiyoyin firimiya.

“Muna cikin waɗanda muka fi iya taka leda a gasar Firimiya, kamar yadda Ten Hag ya sanar wa manema labarai.

“Muna samun damarmaki a lokacin wasa, sakamakon qwallo mai ban sha’awa da muke yi a kakar nan, kuma kowacce ƙungiya kan barar da dama.”

United tana mataki na shida a kan teburin Premier bana, wadda ta ci wasa 16 daga 32 da ta buga kawo yanzu da canjaras shida aka doke ta wasa 12 da maki 54.

United, wadda ta buga Champions League a bana, amma ba ta kai labari ba daga karawar cikin rukuni ta ci ƙwallo 52 aka zura mata 51 a raga a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Ƙungiyar Old Trafford, wadda ta lashe Carabao Cup a bara, za ta buga wasan karshe a FA Cup ranar 25 Mayun da Manchester City a Wembley.

By Editor