Daga BASHIR ISAH
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya biya tsoffin ma’aikatan jihar bashin giraduti sama da Naira biliyan 4.3 da suke bin gwamnatin jihar tun daga shigar 2011.
Mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, an fara biyan waɗanda lamarin ya shafa haƙƙoƙinsu ne tun a watan Fabrairu bayan kammala tantance su.
Sanarwar da ya fitar ta ce, gwamnatin Zamfara ta biya biliyan N4,337,087,492.06 ga tsafin ma’aikatan jihar da na ƙananan hukumomi da suka yi ritaya.
“A watan Fabrt Gwamna Dauda Lawal ya kafa kwamitin tantance bayanan waɗanda lamarin ya shafa sannan aka biya su bashin giraduti da suke bi tun 2011 a matsayin bangare na ƙoƙarin da yake yi wajen tsaftace aikin gwamnati a jihar.
“Bayan kammala tantance bayanan ma’aikatan da suka yi ritaya a jihar, a nan gwamnati ta gano suna bin bashin biliyan N13.4.
“A kashin farko, na biyu da na uku ma’aikata 1,088 aka bi haƙƙonsu bayan kammala tantance su, kuma abin da ya aka biya ya kai N1,836,836,018.95
“A wannan wata kuwa, an biya tsoffin ma’aikata 284da aka tantance Naira 499,435,942.42 a kashi na huɗu. Wanda yawan kuɗaɗen da aka biya ya kama N2,336,271,961.37.
“Bugu da ƙari, ma’aikatan ƙananan hukumomi da malaman firamare 1,744 da suka yi ritaya tsakanin 2011 da 2018, an biya su N2,000,815,530.69 a cikin rukuni huɗu.
“Biyan kuɗaden giraduti da ke gudana babbar nasara ce wadda ake kyautata zaton za ta taimaka wajen rage wa waɗanda lamarin ya shafa raɗaɗin rayuwa.
“Gwamnatin Gwamna Lawal ta nuna cewa a shirye take ta cika dukkan alƙauran da ta yi wa al’ummar Zamfara.”
