Daga BASHIR ISAH
Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta ce za a kammala aikin layin dogo na Kano-Daura ya zuwa 2025.
Ministan Sufuri, Said Alkali, ya ba da tabbacin hakan ne yayin zantawarsu da manema labarai ranar Juma’a a Abuja bayan ziyarar gani da idon da ya kai inda ayyukan hanyar jirgin ƙasan Kano-Maradi da Kaduna-Kano ke gudana.
A cewar Ministan, wannan aikin na daga cikin muhimman ayyukan da Ma’aikatar ke ƙoƙarin ganin ya kammala don a fara cin moriyarsa.
Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwa mai ɗauke da sa hannun Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar, Muhammad Tahir Zakari.
Yayin ziyarar, Alkali ya nuna gamsuwarsa dangane da ci gaban da aka samu a aikin.
Ya ƙara da cewa, bayan kammalawa, ‘yan Nijeriya za gwammace yin tafiye-tafiye a tsakanin jihohi ta hanyar amfani da jirgin ƙasa saboda sauƙin sha’ani.
