Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An bayyana ɓacewar Bello Bukar Adamu, wani mazaunin Kano kuma jami’in Kamfanin Lantarki na Kano (KEDCO), bayan ya samu kiran gaggawa daga Sadik, matashin da ake kyautata zaton amininsa ne kuma abokin aikinsa a Kamfanin na Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO.
Bayan kwana biyu ne kuma a ka tsinci gawar tasa a wani titi da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a jihar.
Abdullahi Abubakar, ƙanin Bello, ya ce marigayin yana a gida da misalin ƙarfe 12 na daren Lahadi, 5 ga Mayu, 2024, lokacin da Sadiq ya yi masa kira na gaggawa.
Ya ce suna sane da cewa Bello yana da hulɗar aiki da wasu mutane kuma yana da ƙwarin guiwar samun wannan aikin.
Abubakar ya ce, “Bello ya yi matuƙar neman aikin Ma’aikatar Harajin Cikin Gida ta Tarayya. Ya kasance mai ƙauna.
Yana aiki da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Kano (KEDCO) kuma yana son shiga FIRS. Kuma wani ne ke neman tayin masa.
“Lokacin da aka buga masa waya dangane da aikin da aka yi masa, sai ya buƙaci matarsa ta kawo mukullin motarsa ya tafi wurin wanda yake jiransa. Tun daga nan ba mu sake jin ɗuriyarsa ba.
“Tun da bai dawo ranar Lahadi ba. Mun yanke shawarar bin diddigin kiran sa. Maganar ƙarshe da ya yi da mutumin a can gefe ita ce Alhamdulillah. Daga nan muka fahimci cewa an yaudare shi ya yarda cewa tayin ya shirya.
Abdullahi ya ce ’yan uwa sun nemi Bello har abada, amma ba su same shi ba.
Ya ce, “Mun fita nemansa daga ɗakin ajiye gawa zuwa wani; daga wannan asibiti zuwa wancan kuma daga wannan ofishin ‘yan sanda zuwa wancan. Mun je duk inda muke tunanin ana iya ajiye gawa. Amma duk da haka babu inda aka same shi. Mun koma gida a raunane.”
Abdullahi ya ce suna tsammanin an yi garkuwa da ɗan uwansu kuma suna sa ran waɗanda suka sace su nemi kuɗin fansa. Amma babu wanda ya kira su don yin haka.
Ya ƙara da cewa, “A ranar Litinin da ta gabata mun kasance a MTD Kano don sake bin diddigin kiransa na ƙarshe, sai muka samu waya daga wani wanda ya shaida mana cewa an tsinci gawa a ƙaramar hukumar Kumbotso, aka kai ofishin ‘yan sanda; sai kuma asibitin koyarwa na Aminu Kano. Gawar ɗan uwanmu ce. An kashe shi da mugun nufi.
“Da alama an kashe shi ne a ranar Lahadi kuma an ajiye gawarsa a wani wuri a ƙaramar hukumar Kumbotso a jihar Kano.
“Bincike ya shaida cewa Bello ya kira na qarshe da Sadiq wanda suka yi aiki tare a KEDCO. Bisa binciken da ‘yan sanda suka gudanar, an gano Sadiq da hannu cikin lamarin. Daga baya Sadiq ya amsa laifin kashe Bello, duk da cewa ana ci gaba da bincike.

Marigayi Bello
“An gano motarsa daga baya, amma ba a iya samun wayoyinsa ba. Kuma Sadiq ya furta cewa yana da hannu wajen kashe Bello. Amma har yanzu ba mu san su wane ne abokan Sadik ba.”
A ranar Talata ɗaruruwan ‘yan uwa da masu fatan alheri ne suka hallara a Gama B inda aka binne Bello.
Abdullahi ya ce ’yan uwa suna cikin matsanancin alhini domin Bello ya aminta da Sadiq.
Ya ce, “Lokacin da aka kori Sadiq daga KEDCO, Bello ya kira shi ya dawo. Kuma sun yi aiki tare. Lokacin da aka yi wa Bello ƙarin girma, ya tabbatar an maido da Sadiq. Sun yi aiki tare har zuwa rasuwarsa. Mun gan shi a matsayin amintaccen ɗan’uwanmu kuma abokin aikinsa.
“Lokacin da na yi da Bello shi ne ranar Juma’a. Na same shi a gida. Mun halarci bikin jana’izar makwabci tare. Da muka dawo gida, sai ya ce mini wani abu yake jira, wanda ya ce idan abin ya tabbata zai yi babban liyafa. Abin takaici a nan muna makokinsa. Ya tafi har abada. Allah Ya gafarta masa,” Abdullahi ya tuna.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa an kama Sadik kuma ana ci gaba da bincike.
Da aka tuntuɓi mai magana da yawun KEDCO, Bala Sani, ya ce har yanzu ba zai iya cewa komai ba a hukumance, ya ƙara da cewa hukumar za ta gana a ranar Alhamis da yamma.
