ASUU na barazanar shiga yajin aiki bisa rashin kafa majalisun jami’o’i

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta bayyana shirin fara yajin aikin gama-gari a faɗin ƙasar domin nuna adawa da gazawar Gwamnatin Nijeriya na kafa Majalisar Gudanarwar Jami’o’in Tarayya.

A yayin wani taro da aka yi a sakatariyar ASUU ta ƙasa da ke Abuja, Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana takaicinsa kan rashin kafa Majalisar Gudanarwa a dukkan jami’o’in tarayya da sauran batutuwan da ba a warware su ba.

Farfesa Osodeke ya bayyaba cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta samu isasshen lokaci don magance buƙatun ƙungiyar.

A watan Mayun da ya gabata ne gwamnati ta rusa majalisar gudanarwar, lamarin da ya bar jami’o’in ba tare da sa ido sosai ba. Bugu da ƙari, ASUU ta soki ƙarin albashin da aka yi a baya-bayan nan na kashi 35 na malaman jami’o’i da kashi 25 na sauran malaman jami’o’in, wanda a cewarsu bai isa ba tare da bayyana su a matsayin albashin wucin gadi da gwamnati.

Matakin da ASUU ta ɗauka na yajin aikin na nuna rashin jituwar da ke tsakanin ƙungiyar da gwamnati kan harkokin gudanarwa da kuma kuɗaɗen da ake ba jami’o’in tarayyar Nijeriya.

By Editor