Jiragen Fadar Shugaban Ƙasa: Za a gurfanar da Nuhu Ribadu gaban majalisa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Dokokin Nijeriya za ta gayyaci mashawarcin shugaban ƙasa kan al’amuran tsaro Malam Nuhu Ribadu, saboda lalacewar jiragen Fadar Shugaban Ƙasa.

Shugaban kwamitin lura da jiragen fadar shugaban a Majalisar, Satomi Ahmed,  ne ya sanar da hakan.

Alhakin kula da jirgin shugaban ƙasa da mataimakinsa dai ya rataya ne a wuyan mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan al’amuran tsaro.

Honabul Satomi Ahmed ya ce a kwai kasafin na musamman domin kula da jiragen fadar shugaban ƙasa.

Ya ce waɗannan maƙudan kuɗaɗe suna ƙarƙashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ne.

Satomi ya bayyana damuwarsa, da cewa abin kunya ne halin da jiragen shugaban ƙasar ke ciki.

Ya ba da misali da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, ciki har da yadda mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya shiga matsala sanadiyyar lalacewar jirgin, wanda dole sai dai ya yi amfani da jirgin haya domin tafiye-tafiye da suka shafi aikinsa.

Satomi ya ce ya kamata ace Nijeriya na iya  kula da jiragenta, musamman idan aka yi la’akari da nasarorin da ta samu a baya kamar iya samar da kamfanin Nigeria Airways.

By Editor