Tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Lamorde ya kwanta dama

Spread the love

Bayanan da suka cim mana na nuni da cewa, tsohon Shugaban Hukunar EFCC, Ibrahim Lamorde, ya kwanta dama.

Majiyarmu ta ce marigayin ya rasu ne a ƙasar Masar inda ya tafi jinya, kuma ya bar duniya yana da shekara 61.

An haifi marigayin ne a ranar 20 ga Disamban 1962, sannan ya shiga aikin ɗan sanda a 1986 inda ya yi ritaya a matsayin Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda 2021.

A halin rayuwarsa, ya riƙe muƙamin Shugaban EFCC daga 2011 zuwa 2015 bayan da Shugaba Goodluck Jonathan ya tsige Farida Waziri a muƙamin shugabancin hukumar.

By Editor