Babbar Kotu a Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alƙali Amina Adamu Aliyu, ta bai wa Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano umarni a kan su gaggauta fitar da Aminu Bayero daga Fadar Sarkin Nasarawa inda yake da zama a halin yanzu.
Haka nan, Kotun ta ba da umarnin haramta wa Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗun da aka tuɓe, ɗaukar kansu a matsayin sarakai har sai ta surari ƙarar da ke gabanta.
Sauran da hanin ya shafa su ne tuɓaɓɓun sarakunan Bichi da Rano da Gaya da kuma Karaye.
Wannan umarni ya biyo bayan ƙararar da lauyan mai ƙara, Ibrahim Isa Wangida, ya shigar ne mai ɗauke da kwanan wata 27 ga Mayu, 2024.
“Kotu ta ba da umarnin wucin-gadi ga masu kare kansu na 1, 2, 3, 4 da 5, a kan kada su da kansu ko waninsu ya ci gaba da ayyana kansa a matsayin sarkin Kano ko Sarkin Bichi ko Sarkin Gaya ko Sarkin Rano ko kuma Sarkin Karaye har zuwa lokacin da kotu za ta saurari ƙaran da ke gabanta,” in umarnin.
