Shekara ɗaya a kan mulki: Gwamna Lawal ya ƙaddamar da wasu manyan ayyuka a Bakura, Maradu

Spread the love

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya ƙaddamar da muhimman ayyukan cigaban al’umma a yankunan ƙananan hukumomin Bakura da Maradun da ke shiyyar Zamfara ta yamma.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Lawal yake cika shekara ɗaya riƙe da ragamar mulkin jihar ta Zamfara.

Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa, Gwamna Lawal ya kai ziyara ƙananan hukumomi guda uku da suka haɗa da: Mafara da Bakura da kuma Maradun.

Ya ƙara da cewa, yayin ziyarar, Lawal ya nuna damuwa kan halin da ya tarar da Babban Asibitin Ƙaramar Hukumar Talatan Mafara saboda rashin ingnci.

Sanarwar da Idiris ya sanya wa hannu ta ce, Lawal ya kai ziyarar ne bisa rakiyar tsohon Gwamnan Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, inda ya ƙaddamar da Kwalejin Harkokin Noma da Fasaha wadda aka yi wa kwaskwarima a Bakura.

Da yake jawabi, Lawal ya ce an ɗauki matakin bunƙasa kwalejin ne saboda muhimmancin da gwamnatinsa ke bai wa fannin noma da ilimi.

Yayin ziyarar tasa a Ƙaramar Hukumar Maradun kuwa, Gwamna Lawal ya tsaya ya duba aikin gayaran Babban Asibitin Maradun domin tafiya daidai da zamani.

Kazalika, Lawal ya yada zango a yankin Talatan Mafara, inda a nan ya nuna rashin gamsuwarsa kan halin da ya ga Babban Asibitin yanki, wanda nan take ya ba da umarnin yi masa kwaskwarima don bunƙasa shi.

By Editor